Da na ci amanar Geidam gara na mutu — Mai Mala Buni
[ad_1]
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce ba zai taɓa cin amanar ubangidansa na siyasa kuma tsohon gwamnan jihar ba, Ibrahim Geidam, wanda yanzu shi ne Ministan Harkokin ’Yan Sanda.
Buni ya bayyana hakan ne yayin taron zaɓen shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Yobe da ke Damaturu.
Gwamnan ya ce siyasarsa ta fara ne da goyon baya da amincewar Geidam.
Kafin ya zama gwamna, Buni ya taɓa zama Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Siyasa a lokacin mulkin Geidam.
Daga baya kuma ya zama Sakataren jam’iyyar APC na Ƙasa.
“Na gwammace na mutu da na ci amanarsa. Ina matuƙar godiya da rawar da ya taka a siyasata.
“Ba zan taɓa mantawa da inda na fito ba, kuma ba zan taɓa juya baya ga mutumin da ya amince da ni ya kuma goyon min baya ba,” in ji Buni.
Ya ƙara da cewa amana tana da muhimmanci a rayuwarsa ta siyasa, kuma yana son a riƙa tunawa da shi a matsayin mutumin da bai ci amanar kowa.
Gwamnan ya kuma shawarci sabbin mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar a jihar da su kasance masu biyayya da haɗin kai.
A nasa ɓangaren, shugaban Kwamitin Zaɓen Jam’iyyar APC na Jihar, Muttaka Rabe Darma, ya ce an zaɓi sabbin shugabannin jam’iyyar ne ta hanyar yarjejeniya bayan tattaunawa da wakilan jam’iyyar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link