Xi Jinping Da Sauran Shugabannin Kasar Sin Sun Halarci Taron Kaddamar Da Zaman NPC

[ad_1]

An kaddamar da zama na hudu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC karo na 14 da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Maris a Beijing, inda shugaban kasar Xi Jinping, da sauran shugabannin jam’iyyar kwaminis da na kasa suka halarci taron, shi kuma firaministan kasar Li Qiang ya gabatar da rahoto kan aikin gwamnati.

Rahoton ya yi nuni da cewa, a shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba mai dorewa duk da matsin da aka fuskanta. Tattalin arzikin kasar ya kuma habaka ta hanyar da ta dace, inda jimillar GPDn kasar ta kai Yuan tiriliyan 140.19, adadin da ya karu da kaso 5 bisa dari.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata, an kara samun mutane miliyan 12.67 da suka samu guraban ayyukan yi a birane da garuruwan kasar Sin, inda matsakaicin yawan wadanda suka rasa ayyukan yi a birane da garuruwa ya kai kaso 5.2 bisa dari. Bangaren kasuwancin waje ma ya habaka cikin sauri, inda kwalliya ta biya kudin sabulu wajen fadada hanyoyin fitar da hajoji zuwa ketare, kuma an samu daidaito a yawan kudaden da aka kashe da kudin shigar da aka samu. Bugu da kari, an kara samar da tabbaci mai karfi wajen kyautata rayuwar jama’a, inda yawan kudin shigar da jama’a suka samu ya yi daidai da yadda tattalin arzikin kasar ya bunkasa, kuma an ci gaba da samun nasarori wajen kawar da talauci, har ma an aiwatar da manufar soke kudin karatu na shekara daya kafin yara su shiga makarantar firamare, manufar da ta amfana wa yara miliyan 14, tare kuma da tafiyar da tsarin ba da tallafin renon kananan yara, wanda ya amfana wa jarirai da kananan yara sama da miliyan 30 a duk fadin kasar Sin. A bangaren aikin noma kuma, jimillar hatsin da aka girbe a duk fadin kasar Sin ta kai kilogiram biliyan 715. Kazalika, an samu babban ci gaba wajen shawo kan hadduran da aka fuskanta a wasu muhimman fannoni, har ma an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.

Kuma bisa rahoton, kasar Sin na sa ran samun karuwar tattalin arziki da kaso 4.5 zuwa kaso 5 a bana, kuma za ta yi kokarin cimma hakan a aikace.

Muhimman bangarorin da za a mayar da hankali kan su a bana sun hada da adadin rashin aikin yi a birane da ya kai kimanin kaso 5.5, samar da sabbin gurabun ayyukan yi sama da miliyan 12 a birane, da karuwar ma’aunin farashin kayayyaki da kimanin kaso 2, karuwar kudin shiga da bisa la’akari da karuwar tattalin arziki, tabbatar da daidaito a bangaren kudaden da ake kashewa wajen shigo da kayayyaki da kudaden ajiya na kasar, samar da hatsi kimanin ton miliyan 700, da kuma rage fitar da hayakin carbon da kimanin kaso 3.8 kan kowane maki na alkaluman GDP.

A cikin rahoton da ya gabatar kan ayyukan gwamnati a bana, firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce Sin za ta kara fadadawa tare da zurfafa bude kasuwanninta ga kasashen ketare. Ya ce, za a rike manufar cin moriya tare, da fadada bude kasuwannin Sin ga ketare bisa ka’idodin kasa da kasa, da gaggauta tafiyar da tsarin samar da kayayyaki yadda ya kamata a duniya, da kuma amfani da bude kofa don inganta gyare-gyare da ci gaba a cikin gida.

A cewarsa, za a fadada bude kofa dogaro da karfin kasar da yin kirkire-kirkire. Za a mai da hankali kan fannin hidimomi don fadada tsarin shigo da kayayyaki a kasuwannin cikin gida da wuraren bude kofa, da kara fadada gwajin bude kofa a fannoni kamar na sadarwa da fasahar kwayoyin halitta, da asibitoci masu jarin kasashen waje, da kuma fadada bude kofa a fannin dijital a mataki-mataki, da takaita jerin hidimomi da aka haramta shigo da su kasar Sin. Ya ce tabbatar da gina yankin gwaji na fadada bude kofa a fannin hidimomi na kasa, za ta inganta sanya hannu kan karin yarjejeniyoyin ciniki cikin ‘yanci da zuba jari tsakanin yankuna da kuma tsakanin bangarori 2, da kuma gaggauta shiga cikin “Yarjejeniyar hadin kan tattalin arzikin dijital” da kuma “Yarjejeniyar hadin kan kasashen Pacific a dukkan fannoni da samun ci gaba”. Ya ce Sin za ta shiga a dama da ita sosai cikin aikin yi wa WTO kwaskwarima, da kuma kiyayewa da bunkasa tattalin arzikin duniya mai bude kofa. Za ta kuma yi iyakacin kokarin habaka yankunan gwaji na ciniki cikin ‘yanci, da kuma inganta karfin kirkire-kirkire don jagorantar ci gaba, da kuma inganta aikin gina tashar ciniki cikin ‘yanci ta Hainan.

Haka kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, ya dace a yi kokarin raya sabbin sana’o’i da sana’o’in da za su bullo a nan gaba. Ya kamata a yi kirkire-kirkirke ga masana’antu, da bai wa kamfanoni mallakin gwamnatin kasa kwarin gwiwar jagorantar aikin kebe wasu wurare na musamman a zahiri don bunkasa sabbin sana’o’in zamani, wadanda suka shafi samar da abun hada laturoni na semi conductor, da zirga-zirgar ’yan sama-jannati da kumbuna a sararin samaniya, da magunguna, da tattalin arziki mai nasaba da zirga-zirgar jiragen sama da na’urori a kusa da doron kasa da sauransu.

Rahoton ya kuma ce, ya dace a kafa tsarin daidaita karuwar jarin da za a zuba ga bangaren sana’o’in da za su bullo nan gaba da hadarin da ka iya faruwa, don raya irin wadannan sana’o’in wadanda za su shafi makamashi da kimiyya da fasahar quantum, da kirkirarriyar basira wato AI, da fasahar hada kwakwalwar dan Adam da injuna masu kwakwalwa wato Brain Computer Interface, da fasahar sadarwar 6G da sauransu.

Li Qiang ya bayyana cewa, Sin za ta rike manufar gudanar da harkokin waje bisa dogaro da karfinta da zaman lafiya, kuma za ta nace ga hanyar samun ci gaba cikin lumana, kana tana fadada hanyoyin huldar abota ta hadin gwiwa da sauran kasashe, kazalika za ta tsaya tsayin daka kan adawa da babakere da fin nuna karfin tuwo a bangaren siyasa, da kuma kare adalci tsakanin kasa da kasa. Sin tana son hadin gwiwa da al’ummar kasa da kasa, don tabbatar da daidaitaccen ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori a duniya, da tattalin arzikin duniya mai fa’ida ga kowa, da inganta aiwatar da shawarar ci gaban duniya, da kuma shawarar tsaro ta duniya da shawarar wayewar kan duniya har da shawarar tsarin shugabancin duniya. Ban da wannan kuma, za ta shiga a dama da ita a cikin aikin yi wa tsarin shugabancin duniya kwaskwarima, da kuma ingiza tsarin kasa da kasa zuwa ga tafarkin nuna adalci da daidaito, da hada kai don gina kyakkyawar makomar bil adam ta bai daya a duniya, da kuma samar da kyakkyawar makoma ta zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Yayin taron, ‘yan majalisar sun nazarci daftarin shirin raya harkokin tattalin arziki da zaman takewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15 wanda wa’adinsa ya fara daga shekarar 2026 zuwa 2030.

Sun kuma nazarci rahoton aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewa na 2025 da na aiwatar da shirin na 2026, da kuma daftarin shirin raya tattalin arziki da zaman takewa a 2026.

Bugu da kari, sun nazari rahoton aiwatar da kasafin kudin gwamnatin tsakiya da na yankuna na 2025 da na aiwatar da daftarin kasafi na gwamnatin tsakiya da yankuna na 2026, da kuma daftarin kasafin kudin na 2026.

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar Li Hongzhong, ya kuma yi bayani kan daftarin dokar kiyaye muhalli da na inganta hadin kai da wadata tsakanin kabilu da kuma daftarin doka kan tsara ayyukan raya kasa.

A cikin rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Sin Li Qiang ya gabatar a yau, daftarin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 ya bullo da wasu muhimman ma’aunai 20 da suka shafi fannoni daban-daban.

Fannin tattalin arziki ya kunshi wasu ma’aunai uku, ciki har da karuwa, da tsari da kuma inganci. Ya dace yawan karuwar GDPn kasar ya kasance ta hanyar da ta dace, kuma a fitar da su bisa hakikanin halin da ake ciki a kowace shekara. Haka kuma, fannin yin kirkire-kirkire ya kunshi wasu ma’aunai uku, inda aka tsara burin cewa, ya dace matsakaicin yawan kudin da aka zuba a fannin nazari da kirkiro sabbin abubuwa a duk kasar ya karu da sama da kaso 7 bisa dari a kowace shekara. Sai kuma fannin inganta walwalar jama’a da ya kunshi wasu ma’aunai 7, wadanda suka shafi samar da ayyukan yi, samun kudin shiga, ilimi, ganin likita, kiwon lafiya, inganta rayuwar tsoffi da yara da sauransu. Sa’annan fannin samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ya kunshi wasu ma’aunai biyar, da suka shafi rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da kiyaye muhallin halittu. Wato ya kamata a rage fitar da iskar Carbon mai gurbata muhalli da kaso 17 bisa dari na yawan GDPn kasar, da ci gaba da inganta ayyukan samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a wasu muhimman bangarori. Shi kuma fannin tabbatar da tsaro ya kunshi wasu ma’aunai biyu da suka jibanci kwarewar ayyukan girbin abinci da samar da makamashi, da zummar ba da cikakken tabbaci ga tsaron kasa. (Masu fassara: Murtala Zhang, Amina Xu, FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *