Iran Ta Kai Hari Kan Ƙungiyoyin Kurdawa A Iraki Yayin Da Rikici Ke Ƙara Bazuwa

[ad_1]

An sake jin karar fashe-fashe a babban birnin Iran, Tehran, a ranar Alhamis, yayin da gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta kai hari kan wasu kungiyoyin Kurdawa da ke Iraki.

Rikicin da ya fara a ranar Asabar bayan hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila, wadanda suka kashe jagoran addini mafi girma na Iran, ya bazu zuwa sassa da dama na yankin. Lamarin ya jawo matsin tattalin arziki a duniya, tangarda ga harkokin makamashi, da kuma rudani a zirga-zirgar tafiye-tafiye.

Hare-haren ramuwar gayya na Iran ya shafi wasu kasashen makwabtanta na yankin Gulf, wadanda ke daukar bakuncin sansanonin sojojin Amurka. A lokaci guda kuma, Isra’ila ta kai hare-hare a Lebanon tare da tura sojojinta zuwa kan iyaka.

A ranar Alhamis, Tehran ta ce ta kai hari kan wasu kungiyoyin Kurdawa da ke Iraki “masu adawa da gwamnatin musulunci ta Iran (IRGC),” yayin da rahotanni ke cewa Amurka na duba yiwuwar bai wa mayakan Kurdawa makamai domin su kutsa cikin Iran.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *