Zargin Kisan Kiristoci: MURIC ta kai ƙarar Amupitan gaban Majalisa
[ad_1]
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC), ta kai buƙatarta na a cire Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
MURIC da wasu ƙungiyoyin Musulmai na neman a cire Amupitan saboda rubutunsa mai shafuka 80 kan zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
Daraktan Zartarwa na MURIC, Ishaq Akintola, ya ce tun watanni uku da suka gabata suka fara ƙorafi kan cire Amupitan.
A cewarsa har yanzu fadar shugaban ƙasa bata ɗauki mataki a kan lamarin ba.
Ya kuma ce abubuwan da Amupitan ya yi a baya na iya sa jama’a su ƙi amincewa da adalcinsa a zaɓen 2027.
“Tun da fadar shugaban ƙasa ba ta saurari ƙorafe-ƙorafenmu ba, dole mu kai batun gaban Majalisar Dokoki,” in ji Akintola.
Ya ƙara da cewa buƙatar ba ta da alaƙa da addini, amma tana da nasaba da abin da suka kira nuna ƙiyayya ga Musulmai.
A baya Amupitan ya bayar da gudunmawa wajen wallafa littafi mai suna Kisan Najeriya Shiru: Kisan kare dangi a Nijarainda ya rubuta babi kan kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Sannan ya zargi Gwamnatin Tarayya da gaza kare waɗanda abin ya shafa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link