AFCON 2025: Morocco Ta Nemi A Binciki Barazanar Katse Wasa Da Senegal Ta Yi
[ad_1]
Hukumar kwallon kafa ta kasar Morocco ta sanar da niyyarta na daukar matakin shari’a dangane da wasan karshe da tawagar kwallon kafa ta kasar ta buga da takwararta ta kasar Senegal wasansu da kasar Senegal, inda ta bukaci hukumar kallon kafa ta Afirka da hukumar a matakin Duniya FIFA da su gudanar da bincike akan ficewar tawagar kasar Senegal daga filin wasa ana tsaka da fafatawa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Litinin, hukumar ta FRMF (a takaice) ta ce ficewar yan wasan kasar Senegal wadda ta biyo bayan hukuncin da alkalin wasa ya yanke na bayar da bugun daga kai sai mai tsaron raga ga kasar Morocco abu ne mai matukar daure kai, duba da cewa dukkan alkalan wasa da suka hada da na cikin fili da masu kula da na’urar VAR sun amince da hukuncin.
Sanarwar ta ce, “Hukumar Kwallon Kafa ta Royal Morocco za ta ci shigar da kara tsakaninta da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) da FIFA game da ficewar tawagar kasar Senegal daga filin wasa yayinda ake tsaka da buga wasan karshe ranar Lahadi bayan hukuncin alkalin wasa na bayar da bugun fenareti, hukuncin da dukkan alkalai suka tsayu akan dacewarshi.
Wasan karshe, wanda aka gudanar a filin wasa na Stade Mohammed V da ke Rabat ranar Lahadi, ya bar baya da kura sakamakon hatsaniyar da ta barke tsakanin yan wasan kasar Senegal da alkalan wasa bayan bayan an bai wa Morocco mai masaukin baki bugun fenariti a minti na takwas na karin lokaci, cikin rashin gamsuwa kocin Senegal, Pape Thiaw, ya jagoranci yan wasansa suka fice daga filin wasan kafin daga bisani su dawo bayan jami’an tsaro sun shiga tsakani.
[ad_2]
Source link