Manyan Ma’aunan Tattalin Arzikin Sin Sun Karu Daga Janairu Zuwa Fabrairu
[ad_1]
Yau Litinin, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, inda ya yi bayani game da yanayin gudanarwar harkokin tattalin arzikin kasa daga watan Janairu zuwa Fabrairun bana.
A yayin taron, kakakin hukumar kididdigar kasar Sin ya ce, daga watan Janairu zuwa Fabrairun bana, yanayin samar da guraben ayyukan yi da farashin kayayyaki sun kiyaye samun ci gaba ba tare da tangarda ba, a sa’i daya kuma, sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ya bunkasa kamar yadda aka yi fata, hakan ya sa, aka bude wani babi mai kyau ta fuskar tattalin arziki a farkon bana.
Haka zalika, daga watan Janairu zuwa watan Fabrairu, yawan karuwar manyan masana’antun kasa ya kai kaso 6.3 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana, ya karu da kaso 1.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara. Game da sana’ar ba da hidima kuma, ma’aunin samarwa na sana’ar ya karu da kaso 5.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya karu da kaso 0.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara.
Ban da haka kuma, daga watan Janairu zuwa watan Fabrairu, yawan kayayyakin yau da kullum da aka sayar ya kai zunzurutun kudi Yuan biliyan 8607.9, adadin da ya karu da kaso 2.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya karu da kaso 1.9 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Disambar bara. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link