‘Yaƙin Iran zai iya durƙusar da tattalin arziƙin duniya’

[ad_1]



Ministan Makamashi na Qatar, Saad al-Kaabi, ya yi gargaɗin cewa sabon yaƙin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da haɗakar Amurka da Isra’ila na iya durƙusar da tattalin arzikin duniya.

Al-Kaabi ya yi wannan gargaɗin ne a yayin wata tattaunawa da jaridar Financial Times, inda ya ce rikicin na iya kawo tsaiko ga ayyukan haƙo mai da iskar gas a yankin.

Ya yi hasashen cewa idan rikicin ya ƙara tsananta, nan da ’yan kwanaki ƙasashen yankin Gulf na iya dakatar da aikin haƙar mai da iskar gas, lamarin da zai iya hana fitar da makamashi zuwa kasuwannin duniya.

Ministan ya ce idan hakan ta faru, farashin gangar ɗanyen mai na iya kaiwa dala 150, yayin da farashin gas kuma tuni ya ƙaru da sama da kashi 40 cikin 100.

Sa’ad al-Kaabi ya ƙara da cewar ko da a ce za a kawo ƙarshen yaƙin na Iran da Amurka a nan take, za a ɗauki makonni ko ma watanni, kafin Qatar ta iya ci gaba da fitar da makamashi gas zuwa kasuwannin Duniya.

Ya ce hakan ya biyo bayan illar da hare-haren makami mai linzami daga Iran suka yi wa babbar matatar gas ta ƙasar, Ras Laffan Industrial City, wadda ita ce mafi girma a ƙasar.

Duk da cewa Qatar na daga cikin manyan ƙasashen duniya wajen fitar da LNG, kaso kaɗan ne daga cikin gas ɗin da take aikawa nahiyar Turai.

A cewar ministan, Turai na iya fuskantar matsin lamba a kasuwar gas, domin tuni ƙasashen Asiya suka fara sayen yawancin ragowar gas da ke kasuwa sakamakon tasirin yaƙin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *