Sanata Barau Da Haɗin Kan APC A Kano
[ad_1]
Ni a wajena, tsarin dimukuraɗiyya ba wai kawai yana nufin abin da ya shafi yawan lambobin mabiya ba ne kaɗai, za a iya cewa; tsari ne da kuma ya shafi daidaituwar al’amura, yin tsinkaye da haƙurin zama da juna, duk a wani yanayi miƙaƙƙe kuma lafiyayye.
Bari na tafi kai tsaye ga makasudin wannan rubutu nawa, wato abubuwan yabawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ke yi, bayan shigowar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Biyan Biliyan 19 Don Ci Gaba da Aikin Titin Kano–Gwarzo–Dayi — Barau
- Doguwa Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano
Da ganin yadda Sanata Barau ke ta kai-wa-da-komowa kan al’amuran jam’iyyar, ka san lallai babban burinsa shi ne ƙara ƙarfafa jam’iyyar, samun nasararta a zaɓukan 2027 da kuma mayar da APC ɗin abar ƙauna ga kowa da kowa. Musamman saboda nasarar samar da tsayayyun manufofi.
Ai wato jama’a ba su ma gama tsinkewa da lamarin Sanatan ba, sai lokacin da ya faɗa a gaban kowa cewa, shi fa ya sarayar da tasa takarar ta neman gwamna. Ya faɗi hakan ne, kwanan baya kaɗan, lokacin karɓar gwamnan zuwa ga jam’iyyar APC, kuma fa ya yi hakan ne bisa raɗin kansa.
Bai tsaya a nan ba, sai da ya bayyana cewa; yanzu duk ƙarfinsa yana bayan gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, kan ya samu ya sake maimaitawa. Ya kuma umarci dukkan magoya bayansa da su yi haka su ma. Yin hakan kuwa, na daga cikin samun tushen haɗin kai a cikin jam’iyyar.
Idan jama’a ba su manta ba, bayan Sanatan ya bayyana matsayarsa ne kan goyon bayan gwamna Abba, a dai lokacin wancan biki, sai tsohon gwamnan na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, CON, a cikin nasa jawabin ya ce; ya gama magana da dukkanin waɗanda ke son tsayawa takarar ta gwamna, dukkaninsu sun janye aniyar takarar tasu, sun bar wa shi gwamnan mai ci, Abba.
A nan, ina ga ba wai Ganduje ne kaɗai ya kamata a jinjinawa ba, yana da kyau a ce su ma ‘yan takarar an jinjina musu. Domin kuwa, wannan ma wani hobbasa ne na nuna son haɗin kan jam’iyya da neman ƙara ƙarfafa ta da kuma nuni wajen yin biyayya ga tsarin shugabanci.
Waɗanda kowa ke kawowa a kansa da Ganduje ya faɗi waccan magana su ne, mai girma Nasiru Yusuf Gawuna da kuma mai girma Murtala Sule Garo. Gaskiyar zance, dole su ma a jinjina musu. Gaba-ɗayansu, suna nuni da cewa; ita fa harkar, ba fa ta ko-a-mutu-ko-rai ba ce. Idan ma akwai wasu masu son tsayawa takarar, bayan waɗannan, to ba za a iya faɗar sunayensu kai tsaye a ce da wane da wane ne ba. Wannan shi ne gaskiyar zance.
Ni a ganina, jam’iyyar APC da jagororinta, sun yi wa gwamna hakan ne don ya ƙara samun nutsuwa a harkar. Sannan kuma, su ƙara nuna masa cewa, yanzu fa an zama ɗaya, ba tare da wata fargaba ba.
Ina ga wataƙila dalilin ma da ya sa aka fito da wani sabon take kenan, na “Kano First.” Domin nuni da cewa, Kano kaɗai aka sa a gaba, babu maganar wata adawa ko hamayya ko rashin amincewa juna, Kano kawai.
Wani abin da na fara lura da shi kuma shi ne, shi da kansa mai girma gwamna ya fara sakankancewa da tsarin tare da yin abin da ya dace daga ɓangarensa, amma a nawa nazarin fa nake magana.
Mun ga yadda ya rungumi tare da ƙara kyautata tsarin kaso na shugabancin jam’iyya a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi. Ni dai har zuwa yanzu, ban ji wajen da gwamna ya yi katsalandan ba, idan kuma na yi kuskure a gyara min.
A nawa nazarin, gwamna na yin abubuwansa ne yadda ya ɗabi’antu da yin su. Na san dai kowane mutum, yana da irin nasa yanayi da tsarin yadda yake tafiyar da al’amuransa. Babban abin buƙata kawai shi ne, taya juna da addu’a.
Ta fuskar Sanata kuma, da ragowar jagorori, dole ne ka yaba musu ganin yadda suke kai gwauro, su kai mari wajen ƙara ƙarfafa jam’iyyar tare da kyautata harkokin mulki. A dalilin haka, ina ga ba zan yi kaffara ba idan na ce, Sanata Barau, a yadda ake ciki yanzu, na ɗaya daga cikin ƙwaƙwalen da ke yin hoɓɓasar ganin an samu kyakkyawan yanayi da haɗin kai cikin APC a Jihar Kano. Wannan ba-wai-ba-inke.
Idan an kula da kyau, za a iya tuna cewa; daga lokacin da ya bayyana janyewa daga takarar gwamna, sai aka ga ya ƙara ɗaura ɗamara sosai, wajen bayar da amintaccen goyon baya na buƙatar samun nasarar APC da gwamna a wannan kakar zaɓe da take daf da shigowa.
Yanzu misali, mu kalli yadda ya yi rabon ababen hawa ga shugabancin APC daf da amsar gwamna Abba cikin jam’iyyar. Ya rarraba ga shugabannin APC na yankin da yake wakilta, wato Kano ta Arewa. Bai tsaya a nan ba kawai, sai da ya je ya tattaba shugabancin na ragowar shiyyoyin.
Wannan fa ba ma a maganar ababen hawa da ya ba wa shugabannin mulki na ƙananan hukumomi 13 na yankinsa na Kano ta Arewa ba. Daf da zan yi wannan fassara ta rubutuna daga Turanci zuwa Hausa, na ji an ce; ya ƙara yin ruwan saman ababen hawa ga shugabannin ƙananan hukumomin shiyyarsa. Wato ko shakka babu, wasu kayan sai amale!
Duk kuma fa abubuwan alherin nan da yake yi, yana yi ne ga kowa da kowa. Babu ruwansa da cewar wai waɗannan tsofaffin ‘yan APC ne, ko kuma waɗancan su ne sabbin ‘yan APC da suka shigo kwanan nan da gwamna. Shi a wajen Barau, dukkansu ɗaya suke, tun da dai dukkansu yan jam’iyyar APC ne.
Kuma fa wani abin ban sha’awa ga wannan Sanatan shi ne, balagarsa a siyasa ta kai ya fahimci cewa, goyon bayan wani tsari ko tafiya ko yanayi, bisa doron doka, a dimukuraɗiyya halas ne. Haka ma kuma, ya fahimci cewa; yin adawa da ƙalubale da kushen yanayi ko tsari ko wata tafiya, shi ma bisa doron doka da oda, halas ne.
Wani babban abin ban sha’awa kuma da na ci karo da shi shi ne, da yawa daga cikin mutanen ɓangaren gwamna Abba da suka shigo da shi daga NNPP zuwa APC, sun yarda kuma sun sakankance cewa, Sanata Barau da gaske har cikin zuciyarsa yana son ganin samun nasarar gwamnan da gwamnatinsa a wannan tafiya da ake ciki.
Sannan wani babban abin lura kuma shi ne, Sanata Barau ya yarda cewa, samun nasarar gwamna, samun nasarar APC ce baki-ɗaya.
[ad_2]
Source link