Kiwon Awakan Alfarma Na Ƙara Haɓaka A Jihar Kano

[ad_1]

Kiwon Awakai na cikin gida, musamman a Jihar Kano ya fara fusknatar ƙalubale, musamman saboda yadda wasu a ƙauyukan jihar, suka fara raja’a wajen fara kiwon wasu nau’ikan Awaki da aka fi sani da na alfarama.

Kusan za a iya cewa, a ɗaukacin wasu ƙauyukan da ke jihar ta Kano, kiwon Shanu na ɗaya daga cikin fannin da ya yi fice a jihar, duba da cewa; ana samun kuɗaɗen shiga da samar da wadataccen abinci da kuma inganta rayuwar masu kiwonsu.

  • Bukukuwan Ƙarshen Shekara: NSCDC Ta Tura Jami’anta 4,000 Don Tsaro A FCT
  • Abubuwan Da Ya Kamata A Lura Da Su Kafin Fara Kiwon Agwagwa (Geese)

Sai dai, a yanzu fannin kiwon Akuyoyin na alfarama a ƙauyukan jihar, za a iya cewa; ya shiga gaban kiwon na Shanu, musamman duba da cewa; wasu nau’ikan Akuyoyin da ake shigowa da su cikin ƙasar, wasu masu kiwon, sun mayar da hankali wajen kiwata su, musamman domin su sama wa kansu kuɗaɗen shiga masu yawa.

An shafe shekaru ana kiwon Akuyoyi a ƙasar nan, waɗanda akasari ana kiwata su ne, domin cin namansu a gida.

Amma sai dai a yau, akwai wasu nau’ikan na Akuyoyi na daban da aka fi mayar da hankali wajen kiwata su, musamman kamar irin nau’ikan Saanen, Damascus da kuma Gulabi waɗanda kuma sun rungumi kiwonsu ne, domin samar da kuɗaɗen shiga.

Akasarin waɗannan nau’ikan na Akuyoyi, masu kuɗi ne suka fi sayen su, domin kiwata su da kuma wasu masu sha’awar yin kiwo.

Ɗaya daga cikin masu kiwata irin waɗannan Akuyoyi, wanda kuma ya kasance ɗaya a kan gaba wajen rungumar kiwata su, mai suna Malam Sunusi Ali Musa, da ke Jihar Kano ya bayyana cewa; kwatsam ya tsinci kansa a cikin sana’ar fara kiwata wannan nau’i na Akuyoyi.

“Mun fara kiwata su ne, a bisa sha’awa kawai, daga baya sai muka lura jama’a sun fara nuna ra’ayinsu na kiwata su, inda ya ƙara da cewa; irin waɗannan Akuyoyin na alfarma, ana kiwata su ne domin kasuwanci a babban mataki” in ji shi.

A cewarsa, ya fara zuba jarin da a kiwata nau’in Saanen, a waɗanda ana shigo da su ne daga Gabas ta Tsakiya, kuma ana samun nono a jikinsu mai yawan gaske.

Ya ƙara da cewa, wasu na sayen nononsu, domin sarrafa shi zuwa magunguna, inda kuma wasu ke kiwata irin waɗannan Akuyoyi domin ado a gida.

Shi ma wani wanda ya rungumi irin wannan kiwo, mai suna Malam Isma’ila Ahmad, a yanzu nau’in Akuyar na Damascus, shi ne ya fi yin tashe kuma suna samar da ingantaccen nama.

Kazalika, Ahmad ya kuma bayyana wani nau’in Akuwar wanda ake kira da Gulabi, kuma akasarinsu farare ne da aka shigo da su daga ƙasar Pakistan.

Samun irin waɗannan nau’ikan na Akuya, ba abu ne mai sauƙi ba, kuma akasarinsu ana safarar su ne daga ƙasashe kamar irin su Libiya da Jamhuriyar Nijar.

An ruwaito cewa, nau’in Akuya na Damascus ana sayar da su ne a kan naira miliyan 3.5, inda kuma nau’in Gulabi ake sayar da su a kan naira miliyan 3 .

Wasu daga cikin masu sana’ar, Alhaji Usman Baba Gara, ya bayyana cewa; kiwon irin waɗannan Akuyoyin a Jihar Kano, na ƙara tumbatsa, musamman ganin cewa, ana samun riba mai yawa, wanda hakan ya sanya ake ƙara samun wasu masu son shiga fannin kiwon nasu.

Sai dai, ya yi gargaɗin cewa; dole ne ga duk mai son kiwata su ya tabbatar da yana bin ƙa’aida, musamman domin kare su daga kamuwa da cututtuka daban-daban.

Bugu da ƙari, su ma wasu ƙwararrun likitocin dabbobi a jihar, sun tabbatar da hakan, inda suka sanar da cewa; irin waɗannan Akuyoyin na alfarma, suna buƙatar son kulawa matuƙa da gaske.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *