Soja ya harbe matarsa, ya kashe kansa a Jihar Neja
[ad_1]
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja.
Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.
Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025.
Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan lamari.
“An gano gawar Last Kofur Femi da matarsa ne a cikin dakinsu da ke Block 15, Room 24 na Corporals and Below Quarters a Wawa Cantonment,” in ji Kyaftin Nwankwo.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a cikin sansanin kafin ya nemi izinin zuwa gida domin wasu bukatun kansa, sai daga bisani aka gano gawarsu a gida.
Kyaftin Nwankwo ya ce an ajiye gawar mamatan domin ci gaba da bincike, kuma rundunar sojan na aiki tukuru don gano musabbabin lamarin.
Rundunar Soja ta Najeriya ta bayyana matuƙar baƙin cikinta kan wannan abin takaici, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Kwamandan Rundunar, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana faruwar irin haka a nan gaba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link