Ina yin kira ga yin ƙauna da haɗin kai — Shugaban CAN




Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Gombe, Rev. Fr. Alphonsus Shinga, ya yi kira ga Kiristoci da su rungumi sahihin ma’anar bikin Kirsimeti ta hanyar ƙarfafa ƙauna da karamci da godiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

A cikin saƙon Kirsimetinsa ga Kiristoci, Rev. Fr. Shinga ya bayyana wannan lokaci a matsayin wani muhimmin lokaci mai tsarki da ke tunatar da haihuwar Yesu Almasihu, tare da koyar da darussan tausayi da sadaukarwa da zaman lafiya da juna.

Ya buƙaci Kiristoci da su kasance masu godiya ga Allah bisa ni’imomin da Ya yi musu, tare da raba abin da suke da shi ga marasa galihu, ciki har da maƙwabta da kuma waɗanda ba Kiristoci ba, yana mai jaddada cewa Kirsimeti lokaci ne na yaɗa ƙauna ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ko ƙabila ba.

Shugaban CAN ya kuma amince da irin ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar, inda ya ce duk da raguwar farashin wasu kayayyaki kaɗan, har yanzu iyalai da dama na fama da matsanancin ƙuncin rayuwa.

Ya ƙarfafi Kiristoci da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri, masu fata da kuma yawaita addu’o’i, tare da taimakon juna domin shawo kan waɗannan matsaloli.

Haka zalika, Reɓ. Fr. Shinga ya yi kira ga matasa da su gudanar da bukukuwan Kirsimeti cikin ladabi da kamun kai, bisa koyarwar addinin Kirista, yana gargadi kan rashin ɗa’a wajen sutura, shan giya fiye da kima da sauran munanan ɗabi’u da ka iya ɓata alfarmar bikin.

A ƙarshe, ya yi wa Kiristocin Jihar Gombe fatan murnar Kirsimeti cikin farin ciki da zaman lafiya, tare da yi musu fatan sabuwar shekara mai albarka da cigaba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *