‘Yansanda Sun Cafke Mutum 1,532 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daban A Bauchi
Daga Khalid Idris Doya
Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta kama a ƙalla mutane 1,532 bisa zarginsu da aikata laifukan daban-daban a sassan jihar a cikin shekarar 2025 da muka yi bankwana da ita.
Rundunar ta kuma amshi kesa-kesai har guda 881 a tsawon wannan lokacin, daga cikin wannan adadin kesa-kesai 880 ne ta gurfanar da su a gaban kotuna daban-daban.
- Tinubu Ya Ƙudiri Aniyar Magance Ƙalubalen Nijeriya – Sanata Danbaba Dambuwa
- Tinubu Ya Ƙudiri Aniyar Magance Ƙalubalen Nijeriya – Sanata Danbaba Dambuwa
A cewar ‘yansandan, sun samu nasara kan kesa-kesai 124 waɗanda kotuna suka yanke musu hukunci, yayin da 756 suke kan fuskantar Shari’a a halin yanzu, sai kuma kes guda ɗaya wanda suke kan gudanar da bincike a kansa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar manema labarai da Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib ya fitar a ranar Labara, dangane da nasarorin da hukumar ta cimma a cikin shekara guda a ƙarƙashin Kwamishina, CP Sani-Omolori Aliyu, kan yaƙi da masu aikata laifukan daban-daban a jihar.
SP Habib ya ce jerin nau’ikan masu laifukan da suka kama na nuni da irin azama da jajircewar hukumar ne wajen kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar a kowani lokacin.
Ya yi bayanin cewar an samu nasarorin ne bisa ayyukan sintiri, ayyukan tsaro, kai samame wuraren da aka gano ‘yan ta’adda na zaune, dukka da nufin tsarkake jihar daga ayyukan miyagu masu janyo ta’addanci.
Sanarwar ta ƙara da cewa bisa ayyukan haɗin guiwa a tsakanin sauran hukumomin tsaro, jama’an jihar, masu ruwa da tsaki, ba su rahoto a kan lokaci suna daga cikin hanyoyin da suka taimaka wa hukumar wajen kyautata ayyukan tsaro a jihar.
Dangane da makaman da suka kamo kuwa, ya ce sun cafke bindiga ƙirar AK-47 guda 6, wata bindiga ƙirar gida AK-47, harbi-ka-noƙe guda 12, fistol ƙirar gida gida 7, wasu nau’ikan bindiga ƙirar gida gida 6, alburusai masu rai guda 352, jakar harsasai masu rai 16 da kuma magazines guda 7.
Kazalika motoci guda 5 da Babura 16 ne aka kamo a tsawon wannan lokacin.
Sauran kayayyakin da aka kwato sun haɗa da takardar kuɗi na N1,000 guda 220 da ake zargin jabun ne, dala guda 5 nau’in dala-100 da ake zargi na jabu ne, wayoyin hannu guda 42 da aka kwato a cikin gida da kuma na fashi da makami, da tufafi guda huɗu masu ɗauke da jini da kuma sanduna 21 da ke da alaƙa da zargin aikata laifin kisan kai.
Sauran sun haɗa da adduna 43, gatari 3, da wani gatari 1 da ke da alaƙa da kisan kai da ƙungiyar asiri.
An kwato kwamfutoci 4 a cikin kesa-kesan fashi da makami, wasu adadin tabar wiwi, Tramadol tablets, wayoyin wutar lantarki, da kuma Filaya (pliers) guda uku an gano su a cikin ayyukan da ake zargin ana lalata ƙadarorin mutane ne.
Har-ila-yau, rundunar ‘yansandan jihar ta kuma kwato shanu guda 12 a tsawon wannan lokaci.
A cewar rundunar a cikin shekara guda an ƙiyasce ƙadarorin da aka yi asararsu sun kai na Naira miliyan 129.8, yayin da kuma adadin ƙadarorin da aka samu nasarar kwatowa sun kai na Naira miliyan 54.2.
SP Nafiu Habib ya bada tabbacin cewar a shekarar 2026 rundunar za ta ƙada jan ɗamara domin yaƙi da masu aikata laifuka tare da tabbatar da inganta kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar. Sun kuma nemi ƙarin haɗin kan jama’an jihar domin cimma nasarorin ayyukan da suka sanya a gaba.