Nijeriya Ta Cigaba Da Zama A Matsayi Na 38 A Jadawalin Iya Taka Leda Na FIFA
[ad_1]
Daga Rabilu Sanusi Bena
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta ci gaba da zama a matsayi na 38 a cikin jadawalin iya taka leda na maza da Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta fitar na baya-bayan nan, an sabunta jadawalin a ranar Litinin yayinda ake gab da shiga sabuwar shekarar 2026, Super Eagles ta kasance a matsayin tun daga watan Nuwamba, lokacin da suka sami jimillar maki 1,502 a zaben da aka yi.
Super Eagles, wadanda a halin yanzu suke Morocco don bugu gasar karo na 35 na kasashen nahiyar Afirika da hukumar AFCON ke shiryawa, suna biye da kasashen Morocco, Senegal, Masar, da Algeria, a matsayin kasashen Afirka a cikin jerin jadawalin na hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA).
Morocco har yanzu ita ce kasar farko a Afirka, wacce take matsayi na 11 a matakin Duniya, yayin da Senegal take matsayi na 19 a duniya kuma take ta biyu a Afirika, kasar Aljeriya ce ke matsayi na uku a Afirika ta 34 a Duniya yayinda kasar Masar wadda ke matsayi na 35 a Duniya ke bi mata, sai Nijeriya dake matsayi na 38 a Duniya kuma matsayi na 5 a Afirika.
Sauran kasashen sune Tunisiya, wacce take matsayi na 41 a duniya, Côte d’Ivoire, tana matsayi na 42, Mali, tana matsayi na 53, Dimokuradiyar Congo, tana matsayi na 56, da Kamaru, wacce take matsayi na 57, suna cikin kasashe 10 da suka fi iya taka leda a nahiyar Afirka.
[ad_2]
Source link