AFCON 2025: Afirka Ta Kudu Ta Doke Angola Da Ci 2-1

[ad_1]

Daga Rabilu Sanusi Bena

Afirka ta Kudu ta doke abokiyar karawarta Angola da ci 2-1 a wasan farko na rukunin B na gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2025 (AFCON) a filin wasa na Marrakesh ranar Litinin, Bafana Bafana ta fara zura kwallonta ta hannun Oswin Appollis, amma Palancas Negras ya farkewa Angola kafin zuwa hutun rabin lokaci.

Duk da haka, yaran na Hugo Broos sun zage damtse wajen ganin sunyi nasara a wasan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida ta hannun Lyle Foster a minti na 80, wasan da Afirka ta Kudu ta yi a rabin lokaci ya cancanci a ci mata kwallo, kuma hakan ya yiwu a minti na 79.

Kasashen za su dawo wasa a ranar Juma’a 26 ga watan Disamba, inda Angola za ta fafata da Zimbabwe, yayin da Afirka ta Kudu za ta fafata da kasar Masar, Afirika Ta Kudu ta Dare saman teburin rukunin B, inda kasar Masar ke matsayi na biyu Zimbabwe a matsayi na uku sai Angola dake matsayi na hudu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *