Ƴansanda Sun Gayyaci Bello Ado Bayero Kan Zargin Damfarar Kuɗin Fili Naira Miliyan 70

[ad_1]

Rundunar ’Yansandan Nijeriya ta shiyyar 1 da ke Kano ta gayyaci Bello Ado Bayero, Hakimin Tarauni kuma ɗan marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, domin amsa tambayoyi kan zargin hannu a wata badaƙalar fili ta Naira miliyan 70. Gayyatar na zuwa ne bayan ƙara tsaurara bincike kan abin da majiyoyi suka kira wata haɗaɗɗiyar hanyar damfarar filaye a Kano.

Kakakin rundunar, DSP Husseini Abdullahi, ya tabbatar da cewa duk mutanen da aka ambata a cikin koken, ciki har da Bello Ado Bayero, an gayyace su domin bincike. Ana zargin Yahaya Mohammed Uba, wanda ake ganin jagoran shirin ne, yana tsare a shalƙwatar shiyyar ta 1.

  • Jam’iyyar NNPP Ta Yi Ɓatan Dabo A Tarkadar Zaɓen Cike Gurbi Na Kano
  • Iyayen Marayu 501 Ne Suka Samu Tallafin Abincin Azumi Daga Dan Amo A Kano

Binciken farko ya nuna cewa an samu mu’amalar kuɗi har Naira miliyan 60 daga asusun Uba zuwa wani asusu da ake alaƙanta shi da Bello Ado Bayero. Koken ya ambaci sunayen Bello Ado Bayero, da Yahaya Mohammed Uba, da Salisu Shuaibu da wani ma’aikacin Hukumar Rijistar Filaye ta Kano a matsayin mambobin ƙungiyar damfarar da ake zargi.

A cewar koken, wani ɗan kasuwa, Alhaji Bashir Mohammed, ya amince ya sayi fili a Darmanawa, ƙaramar hukumar Tarauni, kan Naira miliyan 70 bayan an aiko masa da bayanan asusun banki ta WhatsApp ranar 5 ga Fabrairu, 2026. An ce bayan biyan kuɗin, an shirya ganawar rattaba hannu kan takardu, sai daga baya aka gano takardun bogi ne, yayin da filin ke ƙarƙashin shari’a a babbar kotun tarayya.

Rahotanni sun ce ɗan kasuwar ya nemi a maido masa da kuɗinsa amma hakan bai samu ba, lamarin da ya kai ga shigar da ƙara ga ’yansanda. A halin yanzu, ana ci gaba da tantance bayanan kuɗi da sauran hujjoji domin kammala bincike.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *