An kashe makiyaya 2 a wani sabon hari a Filato




An kashe wasu matasan makiyaya guda biyu a kusa da ƙauyen Jol da ke Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, ya ce an kai wa matasan hari ne yayin da suke kiwon shanu.

Ya ƙara da cewa maharan sun harbe shanu uku har lahira.

Ya bayyana harin a matsayin abun takaici, inda ya ce ya faru ƙasa da sa’o’i 48 bayan wani hari da aka kai yankin Barkin Ladi inda aka kashe makiyaya uku.

Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe da Muhammad Sani da Furuk Bilyaminu.

Ya ce an tona rami aka birne su a ciki, inda jami’an tsaro suka gano gawar ɗaya, yayin da ake neman gawar ɗayan.

Ƙungiyar ta ce ta sanar da hukumomin tsaro game da lamarin, tare da kira ga mambobinta su kwantar da hankalinsu su bi doka yayin da ake ci gaba da bincike.

Ta kuma buƙaci gwamnati ta kare makiyaya da dabbobinsu.

Mai magana da yawun Operation Enduring Peace, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa an tura sojoji zuwa wajen.

Ya ce za a gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.

MACBAN ta zargi wasu daga cikin al’ummar Berom da aikata harin, amma ƙungiyar matasa ta Berom ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta da masaniya kan lamarin.

Wannan sabon hari na nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a wasu sassan jihar.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *