’Yar Wasan Kasar Sin Gu Ailing Ta Kare Kambunta A Gasar Olympics Ta Milan Cortina

[ad_1]

A yau Lahadi, fitacciyar ’yar wasan kasar Sin Gu Ailing ta yi nasarar kare kambunta inda ta lashe lambar zinare a gasar zamiyar kankara ta tsalle da jujjuyawa ta halfpipe, ajin mata a gasar wasannin Olympics ta Milan Cortina. Gu ta yi nasara ne da maki 94.75, bayan ta samu maki 94 wanda shi ne mafi yawa a zagaye na biyu na wasan.

Wannan shi ne lambar zinare na 3 da Gu ta samu a wasannin Olympics bayan 2 da ta samu a wasannin Olympics na Beijing a 2022. Har ila yau, shi ne lambar yabo na 3 da ta samu a wasannin na wannan karo, bayan da ta samu lambar azurfa 2 a wasannin zamiya kan gangare da na tsalle da juyawa a sama.

Li Fanghui ta kasar Sin ce ta lashe lambar azurfa a zagaye na 3 na wasan da maki 93.00 inda Zoe Atkin ta Birtaniya ta samu tagulla da maki 92.50.

Bayan wadannan nasarori, yanzu kasar Sin tana da lambobin zinare 5 da azurfa 4 sai tagulla 6, wannan shi ne sakamako mafi kyau da Sin ta samu a wasannin lokacin hunturu a ketare, bayan zinare 5 da azurfa 2 da tagulla 4 da ta samu a gasar da aka yi a Vancouver a shekarar 2010. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *