“Sabon Karfi Mai Samar Da Bunkasuwa” Yana Da Matukar Muhimmanci

[ad_1]

A shekarun nan, a kan ga bayanan da suka shafi “Sabon karfi mai samar da bunkasuwa” ko kuma “Sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko” cikin manufofin tattalin arziki da gwamnatin kasar Sin ta tsara. Kana wannan nau’in “karfi” na haifar da tasiri mai yakini kan ayyukan raya masana’antu da zaman rayuwar al’umma a kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ne ya gabatar da tunanin da ya shafi “Sabon karfi mai samar da bunkasuwa”. Zuwa yanzu tunanin ya zama ginshikin manufofin kasar Sin, wanda ke tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar cikin inganci. Ta haka za mu iya ganin muhimmancin tunanin, saboda ba ma kawai ya shafi ilimin raya tattalin arziki ba, har ma yana haifar da sauyawar yanayi ta fuskar manufofin bunkasa kasar ta Sin.

Ta hanyar fahimtar ma’anar “Sabon karfi mai samar da bunkasuwa” za mu san me yake haifar da yanayin zamanantar da kasar Sin, da yadda za a gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya a duniyarmu a nan gaba. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *