Mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus
[ad_1]
Kungiyar Kwankwasiyya ta sanar da murabus ɗin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda ya sauka daga kan muƙaminsa a safiyar Juma’a.
A cikin wata sanarwa da Dakta Habibu Sale Mohammed, kakakin Kwankwasiyya ya sanya wa hannu, ya bayyana matakin a matsayin mai wahala amma ya zama dole domin maslahar jama’a da kuma ɗorewar zaman lafiyar gwamnati a jihar.
A cewar sanarwar, wasu yanayi da suka taso a baya-bayan nan ne suka hana Mataimakin Gwamnan sauke nauyin da ya rataya a wuyansa yadda ya kamata, wanda hakan ya sa ya zama wajibi ya bar kujerar domin tafiyar da mulki ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata.
ƙungiyar Kwankwasiyya ta fayyace cewa wannan murabus ba wai yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano take yi masa ba ne.
Sanarwar ta jaddada cewa Mataimakin Gwamnan yana nan a kan bakarsa ta cewa ba shi da laifi, kuma ya yi amanna cewa tarihin ayyukansa a ma’aikatan gwamnati ya nuna gaskiya da kishin jama’a.
Duk da haka sanarwar ta bayyana murabus ɗin a matsayin wani mataki na kishin ƙasa da nufin samar da zaman lafiya, nuna ƙwarewa a fagen siyasa, da kuma kauce wa rura wutar rigingimun da za su iya dakushe ayyukan gwamnati da ci gaba a Kano.
Ta ƙara da cewa, yanzu Mataimakin Gwamnan zai sadaukar da lokacinsa wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya, sake gina tsarin tafiyar, da kuma shiga cikin sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link