An Gudanar Da Liyafar Murnar Bikin Bazara Na Sin Karo Na Farko A Zimbabwe

[ad_1]

Daga ranar 7 zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu, an gudanar da liyafar murnar bikin bazara na kasar Sin na 2026 karo na farko a Harare, babban birnin Zimbabwe, wadda ta jawo hankulan mahalarta kusan dubu 50 da suka hada da ’yan asalin kasar Sin dake zaune a Zimbabwe da al’ummun kasar.

Yayin liyafar, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na shekarar Doki na kasar Sin na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a kan babban dandalin liyafar, wanda ya kara nuna yanayi na haduwa da iyalai da samun ci gaba mai karfi ga liyafar murnar bikin gargajiyar Sinawa da aka gudanar a Afirka.

An nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na shekarar Doki na kasar Sin na CMG a sauran kasashe da yankuna da dama kwanan nan, wadanda suka hada da Birtaniya, Poland, Chile, Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, da sauransu.

Bugu da kari, an gudanar da “taron share fage na shirin talibijin na CMG na murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa” dake Faransa a birnin Marseille na kasar, kuma a gun liyafar murnar bikin bazara na kasar Sin da aka gudanar a ofisoshin jakadancin Sin dake Jamus, New York na Amurka, Calgary na Kanada da sauran wurare, an nuna bidiyon gabatarwar shirye-shiryen bikin bazara na shekarar Doki na kasar Sin na CMG. A sa’i daya kuma, an nuna bidiyon a filin jirgin sama na na kasa da kasa na Auckland dake New Zealand karo na farko.

Ban da haka kuma, an nuna fastocin yayata shirye-shiryen bikin bazara na CMG a kan allon talla mafi girma a tsakiyar Asiya, wato allon ginin kamfanin layin dogo na kasar Kazakhstan, kuma wannan shi ne na tsawon shekaru uku da ake yi a jere.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *