Hatsarin tirela ya kashe mutum 30 a Kano
[ad_1]
Aƙalla mutum 30 ne suka rasu wasu da dama suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Kwanar Barde da ke Ƙaramar Hukumar Gazawa ta Jihar Kano.
Hatsarin ya rutsa ne da wata tirela da ke hanyar zuwa Gujungu da ke Jihar Jigawa a ranar Lahadi.
Rahotanni sun danganta lamarin da tuƙin ganganci da ya yi ajalin mutum 30, wasu da dama kuma suka tsallake rijiya da baya da raunuka.
Gwamnatin Jihar Kano ta tura tawagar jami’an aikin ceto cikin gaggawa zuwa wurin domin kai ɗauki.
Da yake miƙa ta’aziyyarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta jihar da ta kai waɗanda hatsarin ya rutsa da su asibiti tare da kula da su kyauta.
Ya kuma umarci ma’aikatar jin ƙai da ta gudanar da bincike tace da gabatar da miƙa masa rahoto kan ainihin abin da ya faru da kuma tallafin da ya dace ga iyalan mutanen da suka yi hatsarin.
Ya yi addu’ar samun rahama ga mamatan tare da roƙon Allah Ya ba wa iyalan haƙurin jure rashin.
Haka kuma ya buƙaci direbobi da su kasance masu kiyaye dokokin hanya da zumar kare rayukan jama’a da kuma guje wa aukuwar irin haka a nan gaba.
A nasa salon ta’aziyyar, Sanatan Kano ta Arewa kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya yi irin wannan kira, yana mai jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa saurin ɗauka matakan gaggawa musamman na kula da majinyatan kyauta.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link