‘Yan Majalisar Wakilai Sun Nemi A Dakatar Da Aiwatar Da Dokokin Haraji

[ad_1]

Sashin ‘yan majalisar wakilai marasa rinjaye ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da dokokin haraji har sai an kammala bincike, an fayyace gaskiya da kuma tabbatar da dokar da za a aiwatar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Majalisar Wakilai na binciken zargin sauya alƙalami da ake zargin an yi acikin sabbin kundin dokokin haraji da Majalisar Wakilai ta zartar.
Sashin ya kuma nemi goyon bayan dukkanin ‘yan Majalisar don warware yanayin da ke tattare da zargin rashin bin doka da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da masu laifi a gaban ƙuliya domin kare haƙƙoƙin dukkan ‘yan Nijeriya.
‘Yan majalisar sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin wacce shugaban marasa rinjaye, Hon. Kingsley Chinda; mai tsawatarwarta, Hon. Ali Isa J.C; mataimakin shugaban marasa rinjaye, Hon. Aliyu Madaki da mataimakin mai tsawatarwa ga sashin marasa rinjaye, Hon. George Ozodinobi suka sanya wa hannu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *