Gwamnan Kano na shirin komawa APC
[ad_1]
Idan ba a samu sauyi ba, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.
Majiyoyi da dama sun shaida wa wakilinmu cewa gwamnan na iya sauya sheƙa ko da ba tare da yardar uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Bisa ga bayanan cikin gida, Abba ya dage kan sauya sheƙa daga NNPP bayan tattaunawa da manyan ’yan siyasa, ciki har da ’yan majalisar jihar, shugabannin ƙananan hukumomi da wasu ’yan majalisar tarayya daga jihar.
A wani bidiyo da ya bazu a ranar Lahadi, Daraktan Kula da Al’amuran Fadar Gwamna, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya bayyana cewa sun yanke shawarar bin Abba zuwa APC.
Rabo tare da shugabannin jam’iyya a yankinsa, ya ce manyan jiga-jigan Kwankwasiyya a Ƙaramar Hukumar Rogo, sun amince cewa Kwankwaso da Abba su sauya sheƙa.
Ya ce, “Mun yanke wannan shawara ne domin amfanin al’ummarmu, ƙasarmu, har ma da Kwankwaso kansa. Muna ganin burinsa na neman shugabancin ƙasa zai fi samun nasara a APC.”
Rogo ya ƙara da cewa dukkan masu ruwa da tsaki a yankin sun amince da wannan mataki, tare da kira ga magoya baya da su guji siyasar zagi.
A wani bidiyo daban, Darakta-Janar na Yaɗa Labarai a Fadar Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya goyi bayan matakin shugabannin NNPP na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa na bin gwamna zuwa APC.
Shugaban NNPP na Dawakin Tofa, Anas Danmaliki, ya ce Kwankwasiyya ta rabu gida biyu — masu goyon bayan talakawa da masu adawa da su — amma shi da kansilolinsa suna tare da Abba.
Majiyoyi sun ce Gwamna zai sanar da sauya shekarsa a makon farkon watan Janairu.
A gefe guda, Kwankwaso ya kira taron ’yan majalisar jihar a ranar Juma’a, inda ya amince cewa gwamnan na shirin barin NNPP. Ya ce duk wanda ya ga dama ya bi Abba, amma ya nuna rashin gamsuwa da hujjojin sauya sheƙa, yana mai cewa NNPP ta lashe zaben 2023 “da taimakon Allah kaɗai.”
An ruwaito cewa ya tambayi, “Shin Allah da ya ba mu nasara a 2023 ba zai kasance a 2027 ba?”
Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Abba shi ne kaɗai gwamna da NNPP ta samu a zaben 2023.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link