Ɗan Nijeriya Ya Jikkata Yayin da Iran Ta Harba Sabbin Makamai Masu Linzami Zuwa UAE
[ad_1]
An bayyana cewa, aƙalla ɗan Nijeriya ɗaya yana cikin mutane da dama da suka jikkata bayan tare wasu makamai masu linzami na Iran a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a yayin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Mahukunta a ƙasar da ke yankin Gulf sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu yana ci gaba da mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami na ramuwar gayya da Iran ke harbawa tun bayan da rikicin ya fara a ranar 28 ga Fabrairu.
- Rikicin Gabas Ta Tsakiya: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Iran
- NDLEA Ta Kama Mutane 56 A Wuraren Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron UAE ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa rundunonin kariyar sararin samaniyarta sun kirga jimillar makamai masu linzami na ballistic guda 262 da aka harbo daga Iran tun farkon wannan rikici.
A cewar ma’aikatar, 241 daga cikin makaman an samu nasarar tare su, yayin da 19 suka fadi cikin teku.
Sai dai kuma makamai biyu sun faɗa a cikin yankin ƙasar UAE, lamarin da ya haddasa mace-mace da kuma jikkata.
“Wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar mutane shida da suka hada da ‘yan ƙasar UAE, Pakistan, Nepal da Bangladesh, sannan kuma mutane 122 sun samu ƙananan raunuka da matsakaita,” in ji ma’aikatar.
Ta ƙara da cewa mutanen da suka jikkata sun fito ne daga ƙasashe daban-daban da suka haɗa da UAE, Masar, Sudan, Habasha, Philippines, Pakistan, Iran, Indiya, Bangladesh, Sri Lanka, Azerbaijan, Yemen, Uganda, Eritrea, Lebanon, Afghanistan, Bahrain, Comoros, Turkiyya, Iraki, Nepal, Nijeriya, Oman, Jordan da Falasdinu.
[ad_2]
Source link