Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 7 a hanyar Damaturu–Maiduguri
[ad_1]
Wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, ya yi sanadin salwantar rayukan mutane bakwai, yayin da wasu suka jikkata.
Hatsarin ya faru ne tsakanin mota ƙirar Toyota Sienna mai ɗauke da fasinjoji da kuma ƙaramar mota ƙirar Toyota Corolla.
Shaidu, sun bayyana cewa gudun wuce ƙima da direbobin ke yi ne ya haddasa hatsarin.
An ce hatsarin ya auku ne a kusa da ƙauyen Warsala da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Bayan samun labarin hatsarin, jami’an hukumar YEMABUS sun garzaya wajen, inda suka ɗauki gawarwakin da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe (YSUTH) da ke Damaturu.
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Waziri, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutane bakwai sun rasu.
Daga cikin waɗanda suka rasu akwai manya huɗu da yara uku, yayin da wasu suka jikkata.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link