Nijeriya ta doke Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya

[ad_1]



Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis.

Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar lallasa The Panthers har ci 4-1.

Wannan sakamakon ya bai wa Nijeriya nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a wasan cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.

Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78, amma daga baya Gabon ta farke ta hannun Mario Lemina daf a tashi daga fafatawar.

A haka dai aka tashi 1-1 bayan minti 90 da suka buga, lamarin da ya sa aka yi ƙarin minti 30 saboda dole sai an samu wanda zai yi nasara.

Bayan an dawo daga hutun ƙarin lokacin ne aka ci gaba da fafatawar har ta kai ga Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Chidera Ejuke, sannan Victor Osimhen ya ƙara na uku na hudu.

A ɗaya wasan daf da ƙarshen kuma, Kamaru ce za ta fafata da Jamhuriyar Congo a ranar Alhamis, inda duk wanda ya yi nasara a ciki, zai fuskanci tawagar ta Nijeriya a ranar Lahadi mai zuwa.

Wasan na yau dai shi ne na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.

An barje gumin ne ƙasa da awanni 24 bayan tawagar Super Eagles da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) sun warware matsalolin da suka shafi kuɗaɗe tsakanin ‘yan wasa da hukumomin ƙwallon ƙafa.

Kyaftin William Troost-Ekong ya tabbatar da cewa an biya dukkan haƙƙoƙin da suke bi, inda ya ce tawagar ta koma fili cikin karsashi da ƙwarin gwiwar neman nasara a wasan yau.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *