Gidaje fiye da 40 sun lalace a lokacin ruwa da iska

[ad_1]



Mazauna yankin Egbeda Egga da ke ƙaramar hukumar Ijumu a jihar Kogi da dama ne suka rasa matsugunansu, sakamakon iskar guguwa da ta lalata gidajen kwanan mutane sama da 40.

Rahotanni daga yankin a ranar Alhamis sun nuna cewa ruwan saman da ba a yi  tsammani ba a ranakun Talata da Laraba, ya zo ne da guguwa mai ƙarfi wacce ta lalata majami’u, wuraren sana’o’i, da makarantu, inda aka yi asarar dukiya na miliyoyin Nairori.

Shugaban ƙungiyar raya yankin Egbeda-Egga (EDU) na ƙasa, Dakta Emmanuel Dare Otitolaiye, ya bayyana cewa girman ɓarnar ya bar iyalai da dama cikin mawuyacin hali na neman mafita. Ya ce: “Mazauna yankin da dama sun rasa muhallansu, kuma a halin yanzu suna fake ne a gidajen maƙwabta da na ’yan uwa.”

Ya ce: “Mazauna yankin da dama sun rasa matsugunansu, kuma a halin yanzu sun fake ne a gidajen makwabta da na ’yan uwa.”

“Muna kira ga hukumomi da su gaggauta bayar da tallafi ga mutanenmu waɗanda suka rasa gidajensu, sana’o’insu, da hanyoyin neman abincinsu.” In ji shi.

Dakta Otitolaiye ya ƙara jaddada cewa, al’ummar na buƙatar kayan agajin gaggawa, waɗanda suka haɗa da: wurin kwana, abinci da magunguna, domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa su farfaɗo daga wannan ibtila’i .

Haka zalika, ƙungiyar raya yankin Okun (ODA) ta bayyana alhininta game da wannan ibtila’i da ya haifar da gagarumar asara da kuma ƙunci ga mazauna yankin Egbeda-Egga.

ƙungiyar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su samar da matsuguni, abinci da magunguna ga waɗanda wannan ibtila’i ya rutsa da su.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *