Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
[ad_1]
Sojojin rundunar haɗin gwiwa a Arewa maso Gabas sun kashe ’yan ta’addan ISWAP sama da 20, bayan sun daƙile hare-haren da suka kai wa sansaninsu a Goniri, Jihar Yobe.
Sojojin da ke ƙarƙashin Operation Haɗin Kai sun fuskanci hare-hare daga ɓangarori daban-daban a daren 9 ga watan Maris zuwa safiyar 10 ga watan Maris, 2026.
- Gwamna Uba Sani Bai Nuna Goyon Bayan Wani Ɗan Takarar Majalisa Ba – Gwamnatin Kaduna
- Kamfanonin Ketare Na Ganin Sabbin Fa’Idodin Ci Gaba Daga Sabbin Bukatun Kasuwar Sin
A cikin wata sanarwa, jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce an fara gano motsin ’yan ta’addan ta hanyar na’urorin sa ido yayin da suke tahowa daga ƙauyen Goniri da kuma hanyar Ngamdu domin kewaye sansanin sojoji.
Ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa da ƙarfin wuta da dabarun kare kai.
Haka kuma an tura ƙarin sojoji yayin da rundunar sama ta Operation Haɗin Kai ta ba da tallafin kai hare-hare ta sama.
A yayin artabun, ’yan ta’addan sun ja da baya bayan sun yi asara mai yawa.
Fiye da 20 daga cikinsu aka kashe, ciki har da wani babban kwamandansu mai suna Abu Yusu.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da kayayyaki da ’yan ta’addan suka bari yayin da suke tserewa, ciki har da bindigogin ƙirar AK-47, bama-bamai da alburusai iri-iri.
A yayin sintiri a wasu wurare da ke kusa da yankin, ciki har da Gwaigomari a yankin Timbuktu Triangle, an sake gano ƙarin gawarwakin ’yan ta’addan.
Uba ya ce wasu sojoji sun samu raunuka a artabun, amma an kai su asibiti kuma yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.
Ya ƙara da cewa sojoji na ci gaba da riƙe yankin tare da gudanar da bincike a wasu ƙauyukan da ke kusa da yankin, inda ake zargin wasu ’yan ta’addan da suka ji rauni na can.
[ad_2]
Source link