Kotu ta ɗaure mutum 5 kan tone kabari a Gombe
[ad_1]
Babbar Kotun Jihar Gombe, ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin ɗaurin shekaru daban-daban a gidan yari bayan an same su da laifin tone kabari da kuma wasu laifuka da suka shafi sihiri a garin Gadam, da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.
Alƙalin kotun, Abdulsalam Mohammed, ya yanke hukuncin ne bayan an gurfanar da mutanen.
Daga cikin laifukan da ake tuhumar su har da haɗa kai wajen aikata laifi, lalata kabari, sata da kuma mallakar sassan jikin mutum ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mohammed Isah (Chindo), Kawuni Sarki, Manu Saleh, Umar Jibrin (Daddy), da Adamu Nasiru.
Akwai wani mutum mai suna Abdullahi Umar Dauda wanda har yanzu bai shiga hannun jami’an tsaro ba.
Bayanin da aka gabatar a kotu ya nuna cewa a ranar 11 ga watan Satumban 2025, mutanen sun shiga maƙabartar Musulmai ta Gadam cikin dare.
Sun tone kabarin wani mutum marigayi Malam Manu Wanzam.
Ana zargin sun cire idanun mamacin domin amfani da su wajen yin sihiri.
Lauyan gwamnati, Barista Ahmed Yakubu, ya shaida wa kotu cewa laifukan sun saɓa da dokar Penal Code.
A lokacin shari’ar, wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma sun amsa laifukan da aka karanta musu.
Alƙalin kotun ya yanke wa Mohammed Isah da Kawuni Sarki hukuncin shekaru biyar a gidan yari.
Manu Saleh da Umar Jibrin kuma za su yi shekaru biyu da watanni shida, yayin da Adamu Nasiru zai yi shekaru huɗu da watanni shida a gidan yari.
Kotun ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da shari’a kan sauran mutanen da ake zargi da hannu a lamarin amma suka tsere.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link