Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
[ad_1]
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta kammala aikin tantance masaukai da ɗakunan dafa abinci na alhazai a birnin Madinah, a wani ɓangare na shirye-shiryen farko na aikin Hajjin 2026.
Mataimaki na musamman ga shugaban hukumar kan yaɗa labarai, Ahmad Mu’azu, ya bayyana cewa aikin tantancewar ya gudana daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba 2025, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abubakar A. Yagawal, kwamishinan da ke kula da tsare-tsare, da bincike da ƙididdiga.
- NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa
- Hajji: NAHCON Ta Kammala Jigilar Kashi 77 Na Mahajjatan Nijeriya Zuwa Saudiyya
Tawagar tantancewar ta ƙunshi wakilan Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, da mambobin hukumar NAHCON, da jami’an Hukumar jin ɗaɗin alhazai na jihohi. Babban aikin tantancewar shi ne duba shirin duk masu samar da aiyuka, ciki har da binciken kai tsaye kan otal-otal da wuraren dafa abinci, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin NAHCON da na hukumomin Saudiyya game da aminci, da tsafta, da kuma inganci.

A cikin kwanaki ukun, tawagar ta duba otal-otal sama da 20 a yankin Markaziyya da wuraren dafa abinci guda bakwai, inda sakamakon bincike ya nuna cewa an bi ƙa’idojin lafiya da aminci sosai.
Lokacin ƙaddamar da kwamitin a Makkah, shugaban NAHCON kuma babban Jami’in gudanarwa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya jaddada muhimmancin aiki cikin gaskiya, da ɗa’a, da ƙwarewa. Ya ce jin daɗi da kwanciyar hankalin alhazan Nijeriya shi ne babban abin da hukumar ke mayar da hankali a kai.
Farfesa Usman ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin sa ido, da tabbatar da riƙon amana tsakanin masu yin aiki da hukumomi. Ya ƙara da cewa, ana sa ran tawagar za ta mika cikakken rahotonta ga shugabancin hukumar domin nazari da ɗaukar mataki na gaba kafin a kammala shirye-shiryen aikin Hajjin 2026.

[ad_2]
Source link