Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian A Rundunar Sojan Ruwanta

[ad_1]


Kasar Sin ta yi bikin kadammar da babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na yaki, watau CNS Fujian a cikin rundunar sojan ruwanta a ran 5 ga watan nan da muke ciki a birnin Sanya, wanda ya kasance irinsa na farko a Sin mai amfani da na’urar majaujawa wajen cilla jiragen sama ta amfani da wata fasahar mayen karfi mai amfani aiki da lantarki. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin tare da kai ziyara a jirgin.

Shugaba Xi ya kan zura ido sosai kan aikin kera babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na yaki. Ya shiga cikin jirgin bayan bikin don sauraro rahotannin yadda aka gudanar da wannan aiki, da fahimtar karfin yakinsa da yanayin na’urar majaujawar cilla jiragen sama ta amfani da fasahar mayen karfi mai aiki da lantarki da sauransu.

Yi saɓo

Jirgi na CNS Fujian irinsa na farko a kasar Sin dake amfani da wannan fasahar, kuma babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na yaki na 3 a kasar Sin, lambarsa ita ce 18, inda da farko aka fara amfani da shi da kuma rada sunansa a watan Yuni na shekarar 2022. Sin ta dogaro da kanta wajen tsarawa da kera samfurin jirgin na CNS Fujian, sannan fasahar na’urar mayen karfi mai aiki da lantarki da aka sa wa jirgin tana sahun gaba a duniya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *