Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya
[ad_1]
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.
Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.
Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.
Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link