Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi
[ad_1]
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da sauyin musayar kuɗaɗen waje.
A cewarsa, aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa, kum tallafin ya kai ga gidaje miliyan 15.
“Zuwa yanzu, gidaje miliyan 8.5 sun samu aƙalla Naira 25,000 sau ɗaya, wasu kuma sun samu sau biyu ko uku.
“Sauran gidaje miliyan bakwai za su karɓi tallafin kafin ƙarshen shekara,” in ji Edun.
Ya ƙara da cewa ana biyan tallafin ne ta hanyar banki ko asusun wayoyi, ta hanyar amfani da lambar NIN na kowane wanda zai ci gajiyar.
Ministan, ya ce za a ci gaba da saka shirin a cikin kasafin kuɗin shekara-shekara domin ya ɗore.
Shugabar NASSCO, Hajiya Funmi Olotu, ta bayyana cewa dalilin biyan tallafin kashi-kashi, shi ne saboda umarnin Shugaba Bola Tinubu na haɗa tsarin da lambar NIN, domin tabbatar da gaskiya.
“Ba a raba kuɗi a hannu kai tsaye kamar da. Yanzu ana biyan kuɗi ne kai tsaye ta asusun banki. Wannan ne ya sa wasu gidajen suka riga suka karɓi sau ɗaya, biyu ko sau uku,” in ji ta.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link