’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6, sun ƙwato makamai a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami a yankin Pindiga, da ke Ƙaramar Hukumar Akko.

Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama mutanen ne ranar 29 ga watan Janairu, 2026 da misalin ƙarfe 2 na rana, bayan samun bayanan sirri.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Babangida Gamji (shekaru 25), Dahiru Abdullahi (shekaru 30), Ahmadu Garba (shekaru 21), Umaru Bubba wanda aka fi sani da Babuga (shekaru 25), Isah Haruna (shekaru 20) da kuma Usman Abdullahi (shekaru 30).

’Yan sanda sun ce ana zargin ƙungiyar da kai wa wani mutum hari a watan Disamban 2025 a gidansa, inda suka yi ƙoƙarin ƙwace masa babur.

Bayan tsira daga harin, daga baya ’yan fashin sun kira shi a waya suna yi masa barazana tare da buƙatar kuɗi Naira 650,000, wanda tsoro ya sa ya biya su.

Bayan karɓar ƙorafi, ’yan sanda suka fara bincike wanda ya kai ga kama Babangida Gamji da sauran abokan aikinsa guda biyar.

An ƙwato bindiga guda ɗaya, sai bindiga ƙirar gida guda ɗaya, harsasai 12, adda da kuma kuɗi Naira 227,000.

DSP Abdullahi ya ce yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike, yayin da ake ƙoƙarin kamo ɗaya da ya tsere.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Umar Ahmed Chuso, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *