Ɗan Majalisar NNPP Ɗaya Tilo A Bauchi Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC
[ad_1]
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Jama’are, Mubarak Haruna Mai Raƙumi, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
An sanar da sauyin sheƙar ne a yayin wani taron da aka gudanar a ranar Lahadi, 1 ga watan Fabrairu, 2026, inda Mai Rakumi ya zama ɗan majalisa ɗaya tilo daga NNPP a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da ya koma APC, lamarin da ya jawo hankalin manyan ƴan siyasa da magoya bayan jam’iyyun a jihar.
- Gwamnatin Bauchi Za Ta Haramta Haihuwa Ba A Asibiti Ba
- Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi
A jawabinsa, ɗan majalisar ya gode wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon baya da gudummawar da ya ce ya samu daga wajensa a tsawon lokacin da ya shafe a siyasa. Ya bayyana cewa sauyin shekar da ya yi ya biyo bayan nazari da shawara da manyan jiga-jigan mazaɓarsa, domin inganta walwalar al’ummarsa da kuma ci gaban jihar Bauchi gaba ɗaya.
Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa wannan mataki na Mai Rakumi na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a faɗin ƙasar nan, musamman yayin da jam’iyyun ke ƙoƙarin ƙarfafa kansu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
[ad_2]
Source link