Wike Ya Bukaci Bangarorin PDP Su Hada Kai Kafin Zaben 2027
[ad_1]
Sakamakon gagarumin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya kara ruruta rikicin jam’iyyar adawa ta PDP, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar, da su yi watsi da sabanin da ke tsakaninsu da kuma burinsu na sake gina jam’iyyar, gabanin babban zaben 2027.
Da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Wike ya bayyana hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke na tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na soke babban taron jam’iyyar na kasa na 2025, a matsayin wani babban abu mai ma’ana ga PDP.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’addan ISWAP 20 A Jihar Yobe
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 15, Sun Jikkata Da Dama A Katsina
Ya kuma bukaci bangarorin da ke rikici da juna da su kalli hukuncin ba a matsayin wani dalili na ci gaba da shari’a ba, a’a a matsayin wata dama ta sasantawa da sake sabunta jam’iyyar.
“A gare ni, dama ce ga kowa ya sake dawowa, don ganin yadda za mu iya ceto jam’iyyar. Amma ga shi za a fara zaben fidda gwani daga watan Afrilu, yanzu kuma ga shi muna watan Maris.
“Kowa ya bar son zuciyarsa, ka kuma bar abubuwan da kake so, ka dawo mu zauna mu sasanta, domin kuwa wannan dama ce muka sake samu,” in ji shi.
Ministan, wanda bangarensa ke takun-saka da wasu shugabannin jam’iyyar, kan yadda aka gudanar da babban taron da ake takaddama a kai, ya yi gargadin cewa; garzayawa zuwa kotun koli, ba zai bai wa jam’iyyar dama tare da taimakon ta ba, a zabe mai zuwa.
“Idan kun ce kuna son zuwa kotun koli, ku tuna za a yi zaben fidda gwani daga watan Afrilu zuwa na Mayu. Yanzu ku duba, a lokacin da kuka je kotun koli, kawai za ku cutar da kanku kawai, ku kuma cutar da jam’iyyar taku, wanda kuka ce kuna so kuma, wanda ba zai taimaka mana ba ne, “in ji shi.
Wike ya jaddada cewa, shigar kotun ya zama dole, domin batun shugabancin jam’iyyar ya wuce gona da iri, ta hanyar saba ka’idojin tsarin mulki da kuma dokokin zabe.
“Mutane da dama ba su fahimci inda matsalar take ba, ba batun shugabanci muke magana ba, idan kana maganar shugabanci, yanzu kana magana ne a kan harkokin cikin gida.
“Amma lokacin da kuka ce kuna karya kundin tsarin mulki, kuna karya dokar zabe, kuna karya ka’idojin hukumar zabe da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyarku, wannan ba ya cikin harkokin cikin gida na jam’iyya, dole ne kotu ta tsoma baki,” in ji shi.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana gamsuwarsa da matakin da bangaren shari’a ya dauka, inda ya bayyana Juma’a a matsayin daya daga cikin ranakun farin ciki da ya samu a rayuwarsa.
Ya kara da cewa, “Dole ne a koda-yaushe, mu bi ka’ida, a matsayinmu na jam’iyyar adawa, bai kamata mu ki amincewa da hukuncin da aka yi ba.
Wike ya kuma yi amfani da damar wajen nuna mahimmancin jam’iyyar PDP a matsayin dandalin adawa na farko na kasar, inda ya bayyana sauran kananan jam’iyyu da cewa, ba su da wani tasiri.
Da yake yin karin haske kan makomar shugabancin jam’iyyar, Wike ya bayyana cewa; kwamitin riko na jam’iyyar PDP, wanda aka kafa bayan karewar wa’adin jami’an da suka gabata, sun ne halastattun shugabannin da aka sani.
Ya sanar da cewa, tuni kwamitin ya samu amincewar gudanar da sabon babban taron kasa a ranakun 29 da 30 ga watan Maris.
[ad_2]
Source link