’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da kashe ma’aikaciyar Arise TV a Abuja
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, sun kama mutum 12 da ake zargi da hannu a kisan ma’aikaciyar Arise TV, Somtochukwu Christella Maduagwu, a unguwar Katampe da ke Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa Somtochukwu, ta rasu bayan faɗowa daga bene mai hawa uku, yayin da ta ke ƙoƙarin tserewa daga hannun ’yan fashin, yayin da mai gadin gidan ya rasa ransa bayan harbin bindiga.
Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa rundunar Scorpion Squad ƙarƙashin jagorancin ACP Victor O. Godfrey ce ta kama waɗanda ake zargin.
Wasu daga cikin waɗanda aka kama sun amsa laifinsu, inda ɗaya daga cikinsu ya ce shi ne ya harbi mai gadin gidan, yayin da wani ya ce ya yi ƙoƙarin riƙe ’yar jaridar lokacin da za ta faɗo.
Sun kuma bayyana cewa sun sace wata mota ƙirar Honda CR-V mallakin ’yar jaridar, sannan kowa daga cikinsu ya samu Naira 200,000 daga kuɗin da suka sato.
’Yan sanda sun ƙwato bindigogi, harsasai, wuƙaƙe da wayoyi daga hannunsu.
An sake kama wasu daga cikinsu a ranar 8 ga watan Oktoba, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa aikata wani fashin a Maitama.
Kakakin rundunar Abuja, Josephine Adeh, ta ƙi yin bayani kan lamarin, amma Lere Olayinka, mai taimaka wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a shafukansa na sada zumunta.