DSS ta gurfanar da ɗan ta’addan da ya kashe masu ibada a Kogi
[ad_1]
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki a gaban kotu bisa zargin hannu a harin da aka kai a Cocin Deeper Life Bible Church da ke Otite, a Jihar Kogi.
Harin ya auku ne a ranar 7 ga watan Agustan 2012, yayin mutanen ke tsaka da addu’a a cocin.
Mutane uku ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 ne suka buɗe wuta kan masu ibada.
Sama da mutum 19 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ana zargin harin na da alaƙa da ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru.
Bayan harin cocin, ana zargin Obadaki da jagorantar kai hare-hare kan bankuna guda biyar a Uromi, a Jihar Edo.
Yayin kai waɗannan hare-hare, mutane da dama sun rasu, yayin da maharan suka sace kuɗaɗen masu yawa.
Daga bisani jami’an tsaro sun cafke Obadaki tare da tsare shi a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja.
Sai dai ya tsere bayan harin da ’yan ta’adda suka kai Gidan Yarin Kuje a watan Yulin shekarar 2022.
A ranar 15 ga watan Nuwamba, 2025, DSS ta sanar da sake cafke shi.
Bayan shafe kwana shida a hannun hukumar, an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja.
An tuhume shi da laifuka guda shida da suka haɗa da ta’addanci, ƙulla makirci, taimakawa hare-haren ta’addanci, ɓoye bayanai, da tsere wa doka.
Obadaki ya amsa aikata laifi guda ɗaya kacal, wanda ya shafi tserewarsa daga gidan yari.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Janairu, 2026, tare da umartar DSS ta ci gaba da tsare shi, har zuwa ranar sauraron shari’a ta gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link