Tinubu ya isa Maiduguri don ƙaddamar da ayyuka da halartar ɗaurin aure
[ad_1]
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, domin ƙaddamar da wasu ayyuka tare da halartar ɗaurin aure.
Jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin sama na Muhammadu Buhari da ke Maiduguri da misalin ƙarfe 12:58 na rana.
Kamar yadda aka tsara jadawalin ziyarar, Shugaban ƙasar ya je Maiduguri ne domin ƙaddamar da filin jirgin saman ƙasa da ƙasa, tare da wasu ayyuka da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya aiwatar.
Ana kuma sa ran Shugaba Tinubu zai halarci ɗaurin ɗaya daga cikin ’ya’yan tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff.
Za a ɗaura auren a Masallacin Juma’a na Maiduguri, da ke kusa da Fadar Shehu.
Rahotanni daga birnin sun nuna cewa an ƙara tsaurara tsaro a faɗin Maiduguri da kewaye.
Dubban jama’a sun fito kan manyan hanyoyi domin tarbar shugaban ƙasar yayin da ya isa birnin.
Jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban, ciki har da ’Yan Sanda, Sojoji, Sibil Difens, da Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), sun yi tsinke don tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi da wuraren da za a ƙaddamar da ayyukan.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link