Gobarar Kasuwar Gombe; Gidauniya ta ba da tallafin N10m

[ad_1]



Gidauniyar Velocity Humanitarian Foundation ta bayar da gudummawar Naira miliyan 10 ga ’Yan Kasuwar Katako da gobara ta shafa a Gombe, domin rage musu radadin asarar da suka yi.

An miƙa tallafin ne ga shugabannin kasuwar a madadin wanda ya kafa gidauniyar, Injiniya Aliyu Muhammad Kombat, bayan gobarar da ta ƙone shaguna da dama tare da lalata kayayyaki na miliyoyin Naira.

Da yake jawabi yayin miƙa gudummawar, Shugaban gidauniyar, Adamu Aliyu Ibrahim, ya ce sun ziyarci kasuwar ne domin jajanta wa ’yan kasuwar da suka rasa hanyoyin samun abinci sakamakon gobarar.

Ibrahim ya kara da cewa gidauniyar na ci gaba da gudanar da ayyukan jin ƙai a fannoni daban-daban, ciki har da bayar da tallafin lafiya, haƙa rijiyoyin burtsatse, biyan kuɗin makaranta, da kuma taimaka wa marasa galihu da sauran rukunin al’umma masu bukata.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya masu hannu da shuni, musamman ’yan kasuwa a cikin gida da na ƙasashen waje, da su taimaka wa waɗanda masifu suka rutsa da su domin cike giɓin ƙoƙarin gwamnati.

Dangane da yawan aukuwar gobara a kasuwar, shugaban gidauniyar ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su ƙarfafa matakan tsaro, ciki har da samar da cibiyar kashe gobara a cikin kasuwar.

A nasa bangaren, Shugaban Kasuwar Katako, Muhammad Sani Ahmadu, ya bayyana godiyarsa ga gidauniyar bisa wannan taimako na kan lokaci, inda ya bayyana gudummawar a matsayin ceto ga ’yan kasuwar.

“Wannan tallafi ya ba mu ƙwarin gwiwa. Da yawa daga cikinmu mun rasa komai, amma wannan taimako zai taimaka mana mu farfaɗo mu kuma sake fara kasuwancinmu,” in ji shi.

’Yan kasuwar sun kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Gombe da ta samar da cibiyar kashe gobara a cikin kasuwar domin kauce wa sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *