Firaministan Ireland Ya Jaddada Nacewar Kasarsa Ga Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
[ad_1]
Firaministan kasar Ireland Micheal Martin ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin tsakanin raneku 4 zuwa 8 ga watan nan, tsawon shekaru 14 ke nan da firaministan kasar ta Ireland ya sake kawo ziyara kasar Sin, kuma ya zamo shugaban wata kasar turai na farko da ya kawo ziyara a kasar ta Sin a sabuwar shekarar nan.
Yayin zantawarsa da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a kwanan nan, firaminista Martin ya bayyana cewa, “Har kullum muna goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za mu ci gaba da dagewa kan wannan matsayi. Ko da yaushe muna tsayawa kan wannan manufa, kuma ba za mu canja matsayar ba.”
A waje guda kuma, firaministan ya bayyana cewa, “Muna fitar da kaso 90% na kayayyakin da muke kerawa zuwa kasashen ketare. Don haka, mun amince da bin ra’ayin gudanar da budadden tsarin ciniki bisa adalci, da ba da shawarar kafa muhallin gogayya da juna bisa adalci. Kana muna adawa da matakan kara harajin kwastan da kariyar ciniki.” (Mai fassara Bilkisu Xin)
[ad_2]
Source link