Xi Ya Ba Da Amsar Wasikar Malamai Da Dalibai Na Ajin Sinanci Na Makarantar Kasa Da Kasa Ta Faransa

[ad_1]

Kwanan nan, shugaban Sin Xi Jinping ya ba da amsar wasikar malamai da dalibai na ajin Sinanci na makarantar kasa da kasa dake yankin Provence-Alpes-Cote d’Azur na Faransa, inda ya nuna fatan alherinsa gare su da ma dukkan malamai da dalibai na makarantar.

Xi ya bayyana cewa, koyon Sinanci ba ma kawai yana taimakawa wajen fahimtar Sin ba ne wadda kasa ce mai zamanantarwa dake da dogon tarihi, har ma ya ba da taimako wajen gina wata gada zuwa makoma mai kyau ga kasashen Sin da Faransa. Yana maraba da mutane su zo kasar don yin karatu, da ziyara, da kuma yawon shakatawa, ta yadda za su iya fahimtar Sin mai gaskiya, da bude kofa, da kuma kokarin samun ci gaba bisa dogaro da kanta.

Kwanakin baya, wakilan malamai da dalibai daga ajin Sinanci na makarantar kasa da kasa dake Provence-Alpes-Cote d’Azur na Faransa, sun aika wa shugaba Xi Jinping wasika don bayyana ra’ayoyinsu game da koyon Sinanci da kuma sha’awarsu da al’adun kasar.(Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *