Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu
[ad_1]
Dan majalisar zartarwa game da harkokin noma da raya karkara na lardin Gauteng na kasar Afirka ta kudu Vuyiswa Ramokgopa, ya ce manufar nan ta kawar da haraji baki daya kan hajojin kasashen Afirka masu alakar diflomasiyya da Sin, wadanda ake shigarwa babbar kasuwar kasar Sin, za ta haifar da sabbin damammaki, na yaukaka cinikayyar albarkatun gona tsakanin Afirka ta kudu da Sin.
Vuyiswa Ramokgopa, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, a gefen taron baje kolin kasa da kasa dangane da sana’ar kiwon tsuntsayen gida da dabbobi na nahiyar Afirka ko IPLEX.
Jami’in ya kara da cewa, suna maraba da sanarwar jingine harajin da Sin ta ayyana. Ya ce manufar za ta samar da muhimmiyar dama ga kasashen Afirka, musamman Afirka ta kudu, a fannin fadada fitar da hajojinta, da bude sabon babi na ci gaba a muhimman fannoni irin su noma.
Taron baje koli na IPLEX, daya ne daga manyan taruka masu nasaba da sana’ar noma da ake gudanarwa a nahiyar Afirka, wanda ke bayar da damar baje fasahohin kirkire-kirkire na duniya, dangane da kiwon tsuntsayen gida da dabbobi, da kuma sada manoma na gida da masu samar da fasahohin zamani na kasa da kasa, da masu kera kayayyakin noma.
Mahalarta taron na wannan karo sun jaddada cewa, karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin noma, na iya taimakawa wajen karfafa tsarin samar da hajoji a fannin, da fadada damar shiga kasuwanni, da bullo da sabbin damammaki ga manoma, da kasuwancin albarkatun gona a dukkanin sassan nahiyar. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link