Buƙatar Sanya Ƴanmata A Kan Sana’a Kafin Aurar Da Su
[ad_1]
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, wanda yake zaƙulo mana batutuwan da suke ci mana tuwo a kwarya. A yau zan yi magana a kan iyaye mata da maza, Ilimi da kuma sana’a.
A wannan halin da muka tsinci kai ciki cikin wannan lokaci, ilimin ƴaƴa mata yana taimakawa sosai, haka ma sana’arsu. Ya kamata iyaye kafin su aurar da ƴa su tabbatar da sun nema mata waɗannan abubuwa guda biyu, lallai ta yi ilimin addini da na boko. A samu ma na bokon ya fi yawa, kuma kada a ruɗe ku a ce wai ƴar ku kar ta yi ilimin zamani, duk wannan an wuce wannan ‘Jahiliya period’.
- Kuskure Ne Daukar Harkar Fim A Matsayin Sana’a Kadai —Maryam CTV (2)
- Gwamnan Kano Ya Yi Allah-wadai Da Kisan Uwa Da ‘Ya’yanta 6, Ya Umarci A Kamo Masu Laifin
In dai kana da iko da ƙarfi, ƴarka ta yi ilimi sosai, zai taimaketa har zaman aurenta, sannan sana’ar hannu ko ya take a tsaya a koye ta, wannan halin da muke ciki, da ilimin da sana’a zai taimakawa mijinta, ƴaƴanta da ku kanku iyayen.
Saboda wasu a kan tunzurasu cewar da yarinya ta yi sakandari kawai a aurar da ita, wannan karatun me zai amfanar da ita, ba daidai ba ne ba. Likitoci gasu nan, wajen karɓar haihuwa, idan aka ce ƴaƴa mata ba za su yi karutu ba, to maza ne za su riƙa karɓar haihuwa.
Akwai ɓangarori da yawa, idan gida ne yarinyar ta kusa haihuwa, dole ana buƙatar taimakon matan, ba mazan ne za su yi ba. Sannan Ilimi yana da amfani ko da na addini ne, yana da amfani sosai, musamman ɓangaren wankan gawa da sauran abubuwa, yana da kyau a ce ƴaƴa mata suna shiga ɓangaren kada ace komai an barwa maza.
Dole ne mata su mayar da hankali sosai, yana rage lalacewar ƴaƴan zamani, sai an dogara da saurayi ya siya maka waya, ko ya siya miki lesin anko. Idan ki ka yi iliminki ko ki ka yi sana’arki, duk ya ishe ki, wallahi su kansu ƴan’iskan suna tsoron mace mai ilimi, suna tsoron mace mai sana’a, kuma ba za a faɗa mata abu ya ruɗe ta ba.
Dan haka yana da kyau lallai-lallai ilallah idan mata gareka ka nema mata sana’ar da za ta yi, ta dogara da kanta, idan da dama ɗinma makarantar ma ta koma ta ɗan yi, domin za ta taimake ka, za ta taimaki ma ƴaƴanka. Iyaye ma a mayar da wannan hankalin, su kansu samari, ko kafin ka aureta ne, yi ƙoƙari ta yi karatun indai da hali zai taimake ku, ko na bokon ko na addinin.
[ad_2]
Source link