Ja’oji ya yi Allah-wadai da kashe matar aure da ’ya’yanta 6 a Kano

[ad_1]



Hadimin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Zama Ɗan-ƙasa da Jagoranci, Hon. Nasir Bala Aminu Ja’oji, ya yi Allah-wadai da kisan matar aure da ’ya’yanta shida a Jihar Kano.

An kashe Fatima Abubakar mai shekaru 35, tare da ’ya’yanta a gidansu da ke Dorayi Gidan Kwari a ranar Juma’a.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Ja’oji ya bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali, kuma ya ce lamarin ya taɓa zuciyar al’ummar Kano.

“Na shiga matuƙar damuwa da girgiza bisa kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ’ya’yanta shida a Kano.

­“Wannan mugun aiki bai tsaya kan waɗannan mutane ba, ya karya tasirinmu na zaman lafiya da girmama rayuwar ɗan Adam,” in ji shi.

Ja’oji ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayiyar da sauran waɗanda lamarin ya shafa, tare da yin addu’a ga mamatan.

“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan mamatan, da al’ummar Dorayi da Chiranchi, da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano.

“Allah Ya gafarta musu, Ya bai wa iyalansu haƙuri da juriyar jure wannan babban rashi,” in ji shu.

Ya kuma yi kira ga gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da shugabanni da su haɗa kai wajen kare rayuka da hana aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *