Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan

[ad_1]


Kakakin ofishin lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta yi matukar taka-tsantsan game da batun yankin Taiwan.

Chen Binhua, wanda ya yi kiran a Asabar din nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa, dangane da batun shirin Amurka na sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai, na kimanin dalar Amurka miliyan 330, ya ce Sin na matukar adawa da batun sayarwa Taiwan makamai.

Ya ce, “Matsayarmu a fili take kuma ba ta sauya ba. Irin wannan mataki ya yi matukar keta hurumin ‘yancin mulkin kai da tsaron kasar Sin, ya kuma aike da sako marar dacewa, ga ‘yan a-ware masu rajin samun ‘yancin yankin Taiwan.”

Chen Binhua ya kara da cewa, ya kamata bangaren Amurka ya rungumi manufar Sin daya tak a duniya, da sanarwar hadin gwiwa uku da Sin da Amurka suka amincewa, musamman sanarwar ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1982, kuma ta dakatar da tarayya, da goyon bayan sassa masu yunkurin neman ‘yancin kan Taiwan, kana Amurkan ta yi matukar taka-tsantsan dangane da batun yankin na Taiwan.

Ya ce rajin neman ‘yancin kan Taiwan ya saba da dukkanin matakan wanzar da zaman lafiya a zirin Taiwan, don haka Sin ke gargadin gwamnatin jagoran yankin Lai Ching-te, cewa duk wani yunkuri na neman ballewar yankin, ta amfani da goyon bayan wasu sassa na waje, ko karfin soji ba zai yi nasara ba. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *