An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

[ad_1]


An gabatar da rahoton sabuwar taswirar zamanantar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, ta hanyar duba matakai da aka dauka a lardin Hunan na kasar Sin. An gabatar da rahoton ne a jiya Juma’a, yayin babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa, da kwararru, na kawancen Sin da Afirka, wanda ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.

Lardin Hunan ya zama muhimmin wuri na raya hadin gwiwa tsakaninsa da nahiyar Afirka. Bisa kididdigar da hukumar kwastam ta birnin Changsha dake lardin ta fitar, yawan kudin da aka samu daga shige da fice a tsakanin lardin Hunan da nahiyar Afirka a rubu’i uku na farkon shekarar bana ya kai Yuan biliyan 44.52, adadin da ya karu da kaso 19.4 cikin dari kan na makamancin lokaci na bara. A cikin adadin, yawan kudin da aka samu daga fitar da hajoji ya kai Yuan biliyan 21.21, wanda ya karu da kashi 8.3 cikin dari, kana yawan na sashen shigo da hajoji ya kai Yuan biliyan 23.31, wanda ya karu da kashi 31.7 cikin dari.

Rahoton ya shaida cewa, lardin Hunan ya gabatar da tsarin binciken kayan abinci daga Afirka kafin ya shigo kasar Sin, ta yadda za a rika samun izni daga babbar hukumar kwastam ta kasar Sin. A sakamakon hakan, an tsara manufofin musamman don sa kaimi ga samun iznin shigo da kayayyakin amfanin gona, da abinci daga nahiyar Afirka zuwa kasar Sin. Kana lardin Hunan ya kaddamar da yankin gwaji, na cinikin musayar kaya a tsakaninsa da nahiyar Afirka, tare da bayar da inshorar musamman a fannoni da dama.

Ya zuwa karshen watan Oktoba, yawan kudin da aka samu daga cinikin musayar kayayyaki a tsakanin lardin da nahiyar Afirka ya kai Yuan miliyan 204, kana yawansu ya kai matsayin farko a kasar Sin. Haka zalika, hidimar raya tambarin kayayyakin Afirka ta samu nasara, wanda hakan ya sa kaimi ga shigowar karin kayayyakin Afirka cikin kasuwar kasar Sin.

Ya zuwa yanzu, kayayyakin nahiyar Afirka masu tambarori fiye da 120, sun riga sun shiga kasuwar kasar Sin. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *