Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi

[ad_1]



Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi.

An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar.

A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a.

“Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje ba,” in ji tsohon shugaban.

Obasanjo, ya ce cibiyar alama ce ta ci gaba da hangen nesa, wacce za ta taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin Bauchi da sauran sassan duniya.

Ya kuma jaddada cewa babu wata ƙasa da za ta ci gaba ba tare da hulɗa da sauran ƙasashen duniya ba.

Ya bayyana cewa irin wannan gini zai bai wa jihar damar karɓar taruka na ƙasa da ƙasa da kuma janyo hankalin masu zuba jari, wanda hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin Bauchi.

“Idan aka ci gaba da gina wuraren da ke bunƙasa haɗin kai da tattalin arziƙi irin wannan, Najeriya za ta ci gaba da taka rawar gani a fannin ci gaban duniya,” in ji Obasanjo.

A nasa ɓangaren, Gwamna Bala Mohammed, ya gode wa tsohon shugaban ƙasar saboda goyon bayansa, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen bunƙasa ilimi, yawon buɗe ido da ci gaban tattalin arziƙi a jihar.

Ya ce cibiyar za ta zama wajen gudanar da taurkan ilimi, kasuwanci, al’adu da hulɗa tsakanin gida da waje, sannan ta zama shaida ga manufofin gwamnatinsa na mayar da Bauchi cibiyar zuba jari a Arewacin Najeriya.

Wannan katafaren gini na ɗauke da ɗakunan taro daban-daban da aka sanya sunayen tsofaffin gwamnonin Jihar Bauchi.

Ga hotunan yadda taron ya gudana:


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *