Babu Janar ɗin da ISWAP ta kama a Borno — Sojoji

[ad_1]



Rundunar Soji ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da kwamandan Bitget ta 25 da ke Jihar Borno a wani harin kwanton ɓaunan mayaƙan ƙungiyar ISWAP.

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da wannan labarin ƙarya, tare da yin addu’ar samun nasarar sojojin Najeriya da ke bakin daga.

Rundunar ta ce sojojin sun murƙushe wani harin kwanton ɓauna da ISWAP ta kai musu a yayin da suke sintiri domin kare al’ummomin da ke kewaye da Wajiroko a yankin Azir Multe a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

Ta ce sojojin sun gamu da kwanton ɓauna ne daga ’yan ta’adda yayin da suke dawowa daga aikin sintiri a gefen Dajin Sambisa.

Rundunar ta jaddada cewa Kwamandan Brigedi ta 25, Birgediya Janar M. Uba, shi ne ya jagoranci tawagar, wacce ta haɗa da mambobin CJTF, kuma sun koma sansaninsu lafiya.

Ta ce sojojin sun fuskanci harin ne cikin ƙwazo, inda suka yi musayar wuta da makiya har suka fatattake su.

Sanarwar rundunar, ta hannun muƙaddashin kakakinta, Laftanar-Kanar Appolonia Anele, ta ce a yayin arangamar, sojoji biyu da mambobin CJTF biyu sun kwanta dama.

Hedikwatar tsaro ta yaba da jarumtakar dakarun, tare da yin ta’aziyya ga iyalai da abokan aikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu, ya jinjina wa jarumtar dakarun da ke ci gaba da aiki a ɗaya daga cikin yankunan da suka fi haɗari a ƙasar, yana mai cewa sadaukarwarsu abin karramawa ne a kullum wajen kare Najeriya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *