Sojoji sun kashe ’yan ta’adda, sun kama mutum 94
[ad_1]
Dakarun Sojin Najeriya, sun ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a faɗin ƙasar nan, domin murƙushe ’yan ta’adda a yankunan daban-daban.
A cikin makonni biyu da suka wuce, sojoji sun kashe ’yan ta’adda da dama, sun cafke mutum 94, kuma sun ceto 67 da aka yi garkuwa da su.
Daraktan Hulɗar da Jama’a na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Olatokunbo Bello ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja, yayin da yake bayyana rahoton ayyukan rundunar daga 3 zuwa 14 ga watan Nuwamba.
Ya ce sojoji sun ƙwato bindigogi masunyawa, ciki har da rokoki, bindigogi ƙirar gida, da kayan haɗa bam.
Hakazalika, ya ce sun lalata sansanonin ’yan ta’adda da wuraren da ake ƙera musu makamai.
Arewa Maso Gabas
A Jihohin Borno da Adamawa, sojojin Operation Haɗin Kai, sun ci gaba da fatattakar Boko Haram da ISWAP, inda suka kashe adadi mai yawa.
Haka kuma sun kama mutane 45 da ake zargin su da bai wa ’yan ta’adda bayanai da makamai, sannan sun ceto mutum ɗaya da aka sace.
Arewa Maso Yamma
A ƙarƙashin Operation Fagge Yamma, sojoji sun kashe ’yan ta’adda da yawa a Jihohin Sakkwato, Zamfara, Neja, Katsina, Kebbi da Kano.
Sun kama mutum biyu, sun kuma ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato makamai, motocci da dabbobi.
Arewa ta Tsakiya
A Jihohin Filato da Kaduna, sojoji sun yi artabu tare da kashe mahara, sun kama mutum 16, sannan sun ceto mutum biyar.
Haka kuma, sun kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Ibrahim Wakili a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna a ranar 9 ga watan Nuwamba.
Sauran Hare-hare
A Jihohin Kogi, Kwara, Binuwai, Nasarawa da Taraba, sojojin Operation Whirl Stroke, sun kashe ’yan ta’adda da dama, sun kama mutum 10, sannan suka ceto mutun 48 da aka sace.
Sun kuma kama wasu da ke yin safarar makamai da masu taimaka wa ƙungiyoyin ta’adda guda biyu a Nasarawa.
A yankin Neja Delta kuwa, sojojin Operation Delta Safe, sun daƙile yunƙurin satar mai da darajarsa ta kai Naira miliyan 15.8.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link